Da duminsa: Buhari ya mika bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro ga majalisa

Da duminsa: Buhari ya mika bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro ga majalisa

- Buhari ya mika wasika dauke da bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro ga majalisar tarayya

- Kamar yadda wasikar mai kwanan wata 27 ga Janairu ta nuna, an yi wasikar ne ga Ahmad Lawan

- A ranar Talatar da ta gabata ne shugaba Buhari ya sauya hafasohin tsaron kasar nan saboda gawurta rashin tsaro

Shugaban kasa Muhaammadu Buhari ya mika wasika dauke da bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaron da ya nada ga majalisar tarayyar kasar nan.

Kamar yadda takardar da ta samu sa hannun mai bada shawara na musamman ga shugaban kasan a kan harkokin majalisar, Babajide Omoworare ta nuna, wasikar Buhari an yi ta ne ga shugaban majalisa Ahmad Lawan dauke da kwanan wata 27 ga Janairu.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya sanar da nada sabbin hafsoshin tsaron a ranar Talatar da ta gabata, Premium Times ta tabbatar.

KU KARANTA: Shugaban marasa rinjaye tare da wasu 'yan majalisar 6 sun koma APC

Da duminsa: Buhari ya mika bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro ga majalisa
Da duminsa: Buhari ya mika bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro ga majalisa. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

Sun hada da Lucky Irabor mai mukamin Manjo Janar a matsayin shugaban ma'aikatan tsaro, Ibrahim Attahiru mai mukamin manjo janar a matsayin shugaban sojin tudu, Auwal Gambo mai mukamin rear admiral a matsayin shugaban sojin ruwa da Isyaka Amao mai mukamin air vice marshal a matsayin shugaban sojin sama.

Hakan ya biyo bayan cece-kuce da kiraye-kiraye da aka dinga yi ga shugaban kasa a kan ya sallami hafsoshin tsaronsa sakamakon gawurtar rashin tsaro a kasar nan.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya sun yi wa Melaye martani bayan ya wallafa bidiyon asibitin rakuma a Dubai

A wani labari na daban, majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta bai wa sabbin hafsoshin soji da ya nada wa'adin kawo karshen matsalar tsaro, garkuwar da mutane, 'yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da suka addabi kasar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a Abuja a jiya, shugaban kwamitin majalisar a kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce idan Buhari ya samar da abubuwan bukata ga sabbin hafsoshin tsaro, ya basu wa'adi a kan aikin da yake so su yi.

Kamar yadda yace, kada gwamnati ta bata lokaci wurin maye gurbinsu da wasu idan suka gaza, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel