COVID-19: Matar El-Zakzaky ta samu lafiya

COVID-19: Matar El-Zakzaky ta samu lafiya

- Lauyan matar Zeenat El-Zakzaky ta ce ta warka daga cutar korona da ta kamu da shi

- Don haka ta ce a soke umurnin da kotu ta bayar an umurtar hukumar gidan yari ta sake ta

- Lauya mai kare Zeenar, H.G. Magasahi a madadin Femi Falana ne ya nemi kotun ta soke umurnin da ta bada a baya

Lauyoyin matar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar IMN, ya bukaci babban kotun jihar Kaduna ta janye umurnin da ta bada daga baya na umurtar hukumar kula da gidajen gyaran hali sakinta domin jinyar cutar korona, The Vanguard ta ruwaito.

Don haka, kotun ta janye umurnin bayan lauya, H.G. Magashi daga ofishin Falana ya furta wa kotun da baki cewa Zeenah ta warke.

Na warke daga korona: Matar Zakzaky ta ce ba sai an kai ta asibiti ba
Na warke daga korona: Matar Zakzaky ta ce ba sai an kai ta asibiti ba. Hoto: @Vanguardnewsngr
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wadanda Buhari ya naɗa manyan hafsoshin sojoji sun cancanta, in ji Shettima

A cewar Justice Gideon Kurada, "sakamakon bukatar da H.G. Magashi ya shigar da a madadin Femi Falana SAN, masu kare wanda ake kara na farko na biyu Edwin Inegedu Esq suna bukatar kotun ta yi watsi da batun kai wacce ake kara ta biyu zuwa asibiti.

"Lamarin ya canja ne saboda wacce ake kara ta biyu ta warke kuma hukumar kula da gidajen yarin na Kaduna ta bada damar ganin likitocinta. Don haka tana son janye bukatar da ta shigar a ranar 26 ga watan Janairun 2021," in ji shi.

KU KARANTA: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Idan ba a manta a ranar 26 ga watan Janairu, Mai shari'a Kurada ya umurci a saki Matar Zakzaky bayan lauyanta Femi Falana ya gabatarwa kotu rahoton likita sannan ya bukaci kotun ta sake ta domin a yi mata maganin COVID 19 kamar yadda NCDC ta tanada.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164