Bincike ya nuna wiwi zai iya rage yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19

Bincike ya nuna wiwi zai iya rage yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19

- Masana sun nuna fa’idar ganyen wiwi wajen yakar Coronavirus

- An gudanar da wani bincike a kasar Kanada da ya nuna wannan

- COVID-19 ta hallaka mutane fiye da miliyan 2 a kasashen Duniya

Wani sabon nazari da aka gudanar da ganyen wiwi ya nuna tabar za ta iya taimaka wa jiki daga Coronavirus ta hanyar kumbura gabban numfashi.

Jami’o’in Calgary da na Lethbridge da ke kasar Kanada ne su ka gudanar da wannan bincike tare da hadin-gwiwar masu bincike na Pathway Research Inc.

Jaridar Punch ta ce an wallafa sakamakon wannan nazarin kimiyya a mujallar kiwon lafiya Aging.

Wadanda suka gudanar da binciken sun ce ana samun girgizar da ake kira cytokine storms a lokacin da mutum ya fitar da kwayoyin halittar kariya sosai.

KU KARANTA: Babu wani abu a cikin allurar COVID-19 - Gwamnati

Wannan girgiza ta kan jawo mummunan hawan jini, da matsala a hunhu wanda ke kai wa matsalar numfashi a jikin mutum, kamar yadda binciken ya nuna.

Wasu mutanen su kan samu damar yaki da COVID-19 a duk lokacin da jikinsu ya rika fitar da kwayoyin garkuwa da yawa wadanda za su yaki kwayar cutar.

Nazarin da aka gudanar ya nuna mutanen da su ka mutu a sakamakon girgizar da suka samu sun fi wadanda ainihin cutar murar mashakon ta hallaka yawa.

Daya daga cikin wadanda su ka yi wannan bincike, Dr. Igor Kovalchuk na jami’ar Lethbridge da ke garin Alberta, ya ce sam bai yi mamakin abin da suka gani ba.

Bincike ya nuna wiwi zai iya rage yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19
Ganyen wiwi Hoto: www.nutraingredients-asia.com
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari ya jagoranci taron FEC, Ministoci sun yi magana bayan taro

Har a jikin dabbobi, wiwi ya kan rage daskarewar jini, wannan ya na da tasiri ga cutar COVID-19.

Bill Gates ya bai wa Najeriya shawara kan sayen rigakafin COVID-19. Bill Gates ya bayyana cewa Najeriya ba ta bukatar sayen allurar rigakafin a daidai wannan lokaci.

A cewar attajirin Duniya, Bill Gates, inganta asibitoci ya fi sayen rigakafin cutar COVID-19.

Mai kudin ya ce ya kamata a fi mayar da hankali kan farfado da bangaren kiwon lafiya musamman tagayyararrun cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel