FEC ta yarda a batar da N9.44bn a kan gyara tituna da aikin wuta a Najeriya

FEC ta yarda a batar da N9.44bn a kan gyara tituna da aikin wuta a Najeriya

- A jiya ne aka yi taron FEC na majalisar zartarwa da ake yi a kowane mako

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wannan taro a Aso Villa

- Majalisar ta amince da kwangilolin N9.4b da wasu Ministoci su ka gabatar

Majalisar zartarwa ta kasa watau FEC, ta yi na’am da kwangiloli na Naira biliyan 9.44 da za ayi a bangaren wutar lantarki da gyaran tituna a wasu jihohi.

Jaidar Daily Trust ta rahoto wannan a ranar Laraba, 27 ga watan Junairu, 2021, bayan an kammala taron FEC na wannan makon a fadar Aso Rock Villa.

Ministocin tarayya Niyi Adebayo, Lai Mohammed, Babatunde Fashola, da Goddy Jedi-Agba, su ka yi wa manema labarai bayanin abin da su ka tattauna a jiya.

Ministan kasuwanci, Niyi Adebayo, ya bayyana cewa FEC ta amince da kudin wani aikin wutar lantarki da ake yi a Kano, ya ce wannan aiki zai ci N50m.

KU KARANTA: Coronavirus ta sake sa Gwamnati ta hana Ma’aikata zuwa ofis

Tunde Fashola ya yi bayani cewa an amince da N203, 845, 332.50 a matsayin kudin kwangilar zuba na’urorin fasaha a manyan titunan da ma’aikatarsa ta ke yi.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta bada kwangilolin tituna 700 wanda za su ci kilomita 13, 000.

Ministan ya kuma ce an amince da kudin kwangilar gyaran gadar garin Gumi da ruwa ya share da titin Dakitawa a jihar Kebbi da hanyar Gusau zuwa Talata Mafara.

Karamin ministan harkar wutar lantarki, Jedi-Agba ya yi magana da manema labarai game da shirin da ake yi na kafa na’urorin auna shan wuta a gidajen jama'a.

KU KARANTA: Kwanan nan sabon tsarin harajin shigo da motoci zai fara aiki - Hameed Ali

FEC ta yarda a batar da N9.44bn a kan gyara tituna da aikin wuta a Najeriya
Taron FEC Hoto: Twitter @NGRPresident
Asali: Twitter

Lai Mohammed wanda ya yi magana a madadin Ministan Abuja, Mohammed Bello, ya ce an amince da N1, 146, 659, 500 na aikin sa wuta a titin Karshi-Jikwoyi.

Kwanakin baya ne mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bada umarnin bude wasu iyakokin kan tudu hudu a Najeriya, bayan an garkame su tun a 2019.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai bayan kammala wani taron FEC da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Iyakokin da aka bude su ne: Illela (Sokoto), Maigatari (Jigawa), Seme (Legas) da, Mfun (Kuros Riba).

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng