An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa

An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa

- Mata sojoji 300 za su bada gudummawa a yaki da ta'addanci akan hanyar Abuja-Kaduna

- Tuni gwamnan Kaduna, El-Rufai ya karbi 100 daga cikin sojojin tare da bayyana irin kwarin gwiwar da yake da ita akan mata

- Gwamnan ya bayyana cewa aiki da sojoji mata zai taimaka wajen janyo hankalin wasu matan shiga aikin soji

Akalla mata sojoji 300 rundunar soji ta girke don magace ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane, a babban titin Kaduna-Abuja, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya karbi 100 daga cikin sojoji mata 300 ranar Laraba.

An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa
An girke sojoji mata 300 a hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin masu garkuwa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kungiyar tsaffin dalibai na MSS sun nuna kin amincewarsu kan yunkurin rushe masallacin makaranta a Binuwai

Da yake bayani ga sojojin, El-Rufai ya bayyana kwarin gwiwar cewa girke jami'an mata akan babban titin zai kawo karshen rashin tsaro a hanyar.

Gwamnan ya bukaci rundunar soji da ta girke karin jami'ai don karawa sojojin da ke aiki a hanyar karfi don shawo kan garkuwa da mutane a babban titin.

Gwamnan ya ce, "matsalar titin Abuja-Kaduna za ta zo karshe da saboda girke jami'a mata saboda abin da namiji zai yi mace zata iya yin fiye da shi. Mun yadda da ingancin mata a wannan jihar.

KU KARANTA: 'Jami'an tsaro na IPOB sun halaka Hausawa 4 a Imo'

"Ina da yakinin titin zai zama mafi tsaro a Najeriya. Za muyi duk mai yiwuwa don ganin an samu nasarar aikin. Ganin ku zai janyo mata da yawa shiga aikin soja. Shiyasa muke da mace mataimakiyar gwamna don karfafawa wasu matan gwiwa."

Babban kwamandan runduna ta daya, Kaduna, Manjo Janar Usman Mohammed, ya nuna irin jin dadin sa da yadda gwamnatin jihar ke bawa sojoji da sauran jami'an tsaro gudummawa.

Mohammed ya yabawa gwamna El-Rufai da mataimakiyar sa, Dr Hadiza Balarabe, kan yadda suka karbi jami'an da kan su

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel