A mako mai zuwa sabon tsarin harajin shigo da motoci zai soma aiki inji Kwastam

A mako mai zuwa sabon tsarin harajin shigo da motoci zai soma aiki inji Kwastam

- Gwamnatin Tarayya ta rage harajin shigo da motoci a karshen 2020

- Kwastam tace Minista ta ke sauraro, daga nan kudin haraji zai canza

- Hameed Ali yace shi ya nemi shugaba Buhari ya rage harajin motoci

Jaridar Punch tace ana sa ran cewa a makon gobe ne ragin kudin harajin da gwamnatin tarayya ta yi wajen shigo da motoci daga kasar waje zai fara aiki.

Hukumar kwastam mai yaki da masu fasa-kauri a Najeriya ce ta bayyana haka a ranar Talata.

Shugaban hukumar kwastam na kasa, Hameed Ali, ya shaida wa ‘yan jarida a birnin tarayya Abuja cewa suna jiran umarni daga gwamnati a halin yanzu.

Kanal Hameed Ali (mai ritaya) ya bayyana cewa kowane lokaci daga yanzu (a jiya), takarda za ta iya fito wa daga ofishin Ministar tattalin arziki na kasa.

KU KARANTA: COVID-19 ta kashe mutane 1500, an ce Ma’aikata su cigba da aiki daga gida

Hameed Ali ya ce hukumarsa ce ta kawo wannan ragin kudi da aka yi a sabuwar dokar tattalin arziki na shekarar 2020 da shugaban kasa ya sa wa hannu.

Ali ya ce kwastam ta kawo wannan sauyi ne domin a rage tsadar tafiya da zirga-zirga a Najeriya.

“Mu ne mu ka kawo sabon farashin. An yi ta yi mani kaca-kaca, da-dama sun soki hakan, su na cewa na yi amfani da damar da na ke da ita wajen kawo tsarin.”

“Yanzu (ragin harajin) ya zama doka. Mu na jiran Ministar kudi ta bamu umarni a rubuce game da dokar. Daga mun karbi takardar, za mu fara aiki da farashin.”

KU KARANTA: Wata manufar Gwamnatin Trump ta sha kashi a hannun Biden

Shugaban na kwastam ya kara da cewa: “Mu na sa rai zuwa mako mai zuwa, dokar za ta fara aiki.”

A baya kun ji yadda gwamnatin tarayya da Muhammadu Buhari ya ke jagoranta ta kawo sababbin rangawame a sabuwar dokar tattalin arzikin kasa.

Kudirin Finance Act 2020 wanda yanzu ya zama doka ya sa motoci za su rage tsada, an dawo da harajin shigo da motocin waje 10% daga 35% da ake biya a baya.

Da wannan doka da aka kawo babu haraji kan albashin duk ma’aikatan da abin da su ke karba bai wuce N30, 000 ba, kuma an rage nauyin da ke kan kamfanoni.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel