Biyu daga cikin yara 18 da aka dawo dasu daga Anambra 'yan jihar Kano ne

Biyu daga cikin yara 18 da aka dawo dasu daga Anambra 'yan jihar Kano ne

- Biyu daga cikin yaran da aka gano daga jihar Anambra aka kaisu Gombe 'yan asalin Kano ne

- Shugaban kungiyar iyayen yaran Kano da aka sace ya tabbatar da hakan ga manema labarai

- Ya ce sun bi yaran har jihar Anambra inda suka gano cewa daga cikinsu akwai 'ya'yansu

Biyu daga cikin kananan yara 18 da aka kai jihar Gombe daga bisani aka mayar da su jihar Anambra 'yan asalin Kano ne, shugaban kungiyar iyayen da 'ya'yansu suka bace a Kano, Ismail Ibrahim Mohammed ya tabbatar.

A yayin zantawa da Daily Trust, Mohammed ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa a kan lamarin an sanar da su cewa an kai wasu kananan yada Gombe amma su je su duba su gani ko akwai yaran Kano a ciki.

"A yayin tafiyarmu zuwa Anambra, mun gano cewa yara biyar daga ciki an sato su ne daga Kano. Mun sake zuwa Gombe domin kara dubawa," yace.

KU KARANTA: Sai da 'yan daba suka fara harbe-harbe kafin su bankawa gidan Igboho wuta, 'Yan sanda

Biyu daga cikin yara 18 da aka dawo dasu daga Anambra 'yan jihar Kano ne
Biyu daga cikin yara 18 da aka dawo dasu daga Anambra 'yan jihar Kano ne. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

"Muna kokarin komawa Anambra bayan mun gano wasu biyu na daban daga Gombe. Za mu kwaso biyar daga Anambra sai mu hada da biyun Gombe mu mika su hannun iyayensu na asali," yace.

A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta kwatanta canja tsofaffin shugabannin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari yayi a matsayin makararren mataki, don jama'a sun riga sun cutu, Daily Trust ta ruwaito.

PDP ta bukaci a yi gaggawar bincike akan yadda tsofaffin shugabannin tsaron suka tafiyar da ayyukansu lokacin da suke kan kujerunsu, saboda tana zargin suna da hannu dumu-dumu akan satar kudaden da aka ware musamman don tabbatar da walwalar rundunoni a filayen daga.

A wata takarda ta ranar Talata, sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya ce "Daga baya kenan, sadaka da karuwa. A cewarsa sun riga sun janyo rikicewar kasa da asarar rayuka."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel