Zulum ya yi maraba da naɗin sabbin manyan hafsoshin sojoji da Buhari ya yi
- Gwamna Babagana Umara Zulum Zulum ya bayyana jin dadin sa da nada sabbin hafsoshin tsaro tare da godewa na baya
- Gwamnan na Jihar Borno ya tabbatar da cewa ya na da yakinin sabbin hafsoshin za su yi abin da ya dace tare da tabbacin ba su duk goyon bayan da ya dace
- Zulum ya bayyana haka ga wasu manema labarai a Maiduguri lokacin da su ka nemi jin ra'ayin sa game da nada sabbin hafsoshin tsaro
Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya yi maraba da nadin sabbin hafsoshin tsaro, yayin da yake mika godiya ga tsofaffin hafsoshin, musamman babban hafsan sojojin kasa, da na sama, Janar Tukur Buratai da Air Marshall Abubakar Sadique wanda gwamnatin Borno tayi aiki da su hannu da hannu wajen yaki da Boko Haram.
Zulum ya danyi takaitaccen bayani da daren jiya Talata a Maiduguri, lokacin da wasu manema labarai su ka nemi jin ra'ayin sa game da sanarwar da shugaba Muhammadu Buhari ya fitar ranar Talata na sauya manyan hafsoshin sojojin.
Buhari ya nada Manjo Janar L. E. O Irabor a matsayin shugaban rundunar tsaro, Janar Ibrahim Attahiru a matsayin babban hafsan sojin kasa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo a matsayin babban hafsan sojin ruwa da kuma Air Vice Marshal Isiaka Oladayo Amoa a matsayin babban hafsan sojin sama.
DUBA WANNAN: Kungiyar tsaffin dalibai na MSS sun nuna kin amincewarsu kan yunkurin rushe masallacin makaranta a Binuwai
"Munyi aiki da manyan hafsoshin masu barin gado tsawon shekara shida da suka wuce, kuma tsawon wannan lokaci na kalubale, sun bada cikakkiyar gudummawa wajen yakin da muke da Boko Haram.
"Kokarin mu na sake gimawa da daidaita al'amura a fadin jihar Borno bazai kammala ba tare da hadin gwiwar Laftanar Janar Buratai a matsayin hafsan sojojin kasa, Air Marshall Sadique a matsayin babban hafsan sojin sama, da kuma, gudummawar sauran hafsoshin tsaro, jami'ai na musamman, kungiyoyin tsaro da na sa kai.
KU KARANTA: Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya
"Ba za mu manta da irin wannan babbar gudummawa ba, amma kuma, kamar yadda gaba daya muka sani, komai da lokacin sa, muna godiya ga duk hafsoshin masu barin gado a irin gudummawar da suka bayar kuma muna yi musu fatan alheri a sauran rayuwar su.
"Ga sabbin hafsoshin, musamman, Janar L. E. O Irabor wanda shi ne babban hafsan tsaro da Janar Attahiru, babban hafsan soji, duka su biyun sun yi aiki a nan Borno a matsayin kwamandojin Operation Lafiya Dole, sun san matsalar mu kuma na tabbatar za su yi aiki tukuru.
"Gwamnatin Jihar Borno zata basu cikakken goyon baya kamar yadda muka bawa na bayan su, kuma zamu ci gaba da aikin mu wajen taimakawa jami'an tsaro da dabaru wanda mun dade muna yi, za kuma mu ci gaba da daukar jami'an sa kai tare yi wa jami'an tsaro addu'a da tallafawa iyalan su kamar yadda muka saba" in ji Zulum.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng