Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya

Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya

- 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi fulani makiyaya da su kauracewa dazukan yankin Niger Delta

- Sun bayyana hakan cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kare hakkin Ijaw da sakataren sa suka sanya hannu

- Sun bayyana cewa duba da yarabawa suka tsaurara tsaro a yankunan su, su ma ba su ga abin jira ba, dole su kare yankin

Yayin da rani ke tilasta makiyaya da shanun su yin hijira zuwa kudancin kasar, kungiyar kare hakkin Ijaw, Ijaw Unity Watchdog, IUW, ta gargadi fulani makiyaya da su kauracewa dazikan da ke kudu maso kudu da kuma kudu maso gabashin kasar nan, Vanguard ta ruwaito.

Kungiyar a wata sanarwa da ta fitar jiya ta hannun shugaban ta na kasa, Pereotubo Sunny da sakatare, Emmanuel Daarepamowei, sun bayyana rashin jin dadi game da ayyukan ta'addancin Fulani makiyaya a fadin kasar nan tare da gargadin cewa za su yi duk abin da za su iya don kare yankin kudu.

Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya
Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama matasa 'Hausawa' dauke da bindigu a Oyo

Sanarwa wadda aka sanyawa hannu tare da wasu biyu tana cewa: "Muna kira ga Fulani makiyaya da kada su nufi yankin Niger Delta da mummunar akidar su na garkuwa da mazauna yankin, abin ya isa haka, ba ma farin ciki da Fulani makiyaya kuma muna jan kunnen kungiyar gwamnonin Niger Delta, da su hana Fulani makiyaya shigowa yankunan mu.

"Yarbawa suna ta daukan matakan tsaro don kare garuruwan su da kudu maso gabas gaba daya, mai muke jira. Abin da ya shafi dan uwan ka kaima wata rana zai iya samun ka.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna)

"Manyan Niger Delta ku farka, muna da hujjoji da dama da za mu iya gwada irin rashin adalcin da ake wa mutanen Niger Delta, da hakkokin mu da aka danne, amma idan muka hade kan mu a matsayin yan Niger Delta, su waye Fulani makiyaya a kasar nan, mun fi su karfi da ci gaba, dole mu tsaya kan kudirin mu.

"A madadin Fulani Nationalist Movement (FUNAM) muna yi wa gwamnati da hukumominta gargadin su shawarce su. Shugabanni da mambobin Ijawa Unity Watchdog na umurtar fulani da ke dazukan jihar Delta da Bayelsa su fice."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel