Sojoji sun sada ƴan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe

Sojoji sun sada ƴan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe

- Dakarun sojojin Najeriya na cigaba da samun nasara a yakin da suka yi da yan ta'adda a kasar

- Rundunar sojin ta ce sanar da cewa dakarun Dakarun Operation Tura Takaibango sun yi nasarar kashe yan ta'adda a Borno da Yobe

- Sojojin sun kuma yi nasarar kwato bindigu da harsasai yayin da suke cigaba da bin sahun yan ta'addan da suke tsere

Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka 'yan kungiyar Boko Haram guda takwas a wata arangama da suka yi a baya bayan nan a jihohin Borno da Yobe, The Punch ta ruwaito.

Sanarwar da direkta mai rikon kwarya na sashin watsa labarai na rundunar, Brig Janar Benard Onyeuko ya fitar, a ranar Litinin, ta ce sojojin sun yi nasarar taka wa yan ta'adda birki a jihohin Yobe da Borno.

.

Sojoji sun sada yan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe
Sojoji sun sada yan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe. Hoto: @MobilePunch
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya

Sanawar ta ce, "Dakarun Operation Tura Takaibango, wani sashi na Operation Lafiya Dole a Arewa maso Gabas na cigaba da dirkake yan Boko Haram/ISWAP a yayin da suka kai musu hari a mabuyarsu a garin Chindila a Yobe da Mayankari a Borno.

"A ranar 25 ga watan Janairun 2021, misalin karfe 1 na rana, dakarun bataliya ta 233 da ke Babangoda yayin sintiri sun yi arangama da 'yan Boko Haram a kauyen Chindila. Sun bude musu wuta inda suka yi nasarar halaka biyar cikinsu yayinda wasu suka tsere da raunin bindiga.

"Kayayyakin da suka kwato sun hada da; Ak 47 guda 3, harsasahi da alburusai. Sojojin sun bi sahun abokan gaban kuma suna cigaba da mamaye yankunan."

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Buhari ya naɗa Aghughu a matsayin sabon AGF

An kuma kashe 'yan bindiga da dama a wasu kananan hukumomin jihar Kaduna.

Kanananan hukumomin sun hada da Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan a ranar Talata

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel