Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna)

Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna)

- Daya daga cikin gidajen Sunday Igboho mutumin da ya sha alwashin korar makiyaya fulani daga kasar Yarabawa ya kone

- Rahotanni sun bayyana cewa a safiyar yau Talata ne lamarin ya faru

- A halin yanzu ba a tabbatar da ko gobara ce ba ko kuma wasu ne suka cinna wa gidan wuta

Ana zargin wasu bata gari da a yanzu ba a san ko su wanene ba sun kona daya daga cikin gidajen Sunday Igboho mai rajin kare hakkin 'yan kabilar Yarbawa da ya sha alwashin fatattakar makiyaya daga yankin Kudu maso Yamma.

The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata 26 ga watan Janairun 2021.

Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna)
Yanzu Yanzu: An cinnawa gidan Sunday Igboho wuta a Ibadan (Hotuna). Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An cafke uba da ƴaƴan sa biyu a cikin gungun 'yan bindigan Katsina

A halin yanzu ba a tantance irin barnar da wutar ta yi ba kuma ba a samu ji ta bakin Igboho ba ko kuma wata hukumar tsaro game da lamarin.

Sai dai daya daga cikin hadimansa da baya so a bayyana sunansa ya shaidawa The Cable cewa yana zargin wasu da ba su son abinda Sunday ke yi ne suka cinnawa gidan wuta.

A jiya Litinin ne dai kungiyar gwamnonin Najeriya wato NGF karkasshin jagorancin gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi ta jagoranci zaman sulhu tsakanin shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) da gwamnonin yankin Kudu maso Yamma don cimma matsaya.

KU KARANTA: Wata mata ta sheƙawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi a Kano

A karshen taron gwamna Fayemi ya bayyana cewa ba korar makiyaya fulani gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya yi ba kawai cewa ya yi makiyayan da ke son cigaba da kiwo a dazukan jihar su yi rajista.

A cewarsa, rajistan zai bawa gwamnatin damar sanin wadanda ke zaune a dazukan jihar don banbance su daga wasu da ke aikata laifuka da kai hare hare da sunan makiyaya fulani.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel