Mahaifin yaron ya mani ciki ya tsere, shi ya sa na saida jaririna inji ‘Yar shekara 22
- Dakarun Amotekun sun cafke matar da ta saida jaririn da ta haifa a Ondo
- Wannan mata ta karbi N10, 000 a hannun wani Fasto, ta rabu da jaririnta
- Matar ta ce talauci ne ya addabe ta, faston da ya saye jaririn ne ya tona asiri
Wata Baiwar Allah mai shekara 22, Seun Oladayo, wanda ta saida jaririnta a kan kudi N10, 000, ta shaida wa Duniya abin da ya kai ta ga yin wannan aikin kawai.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an kama Seun Oladayo da laifin saida ‘dan cikinta ga wani Fasto a garin Ondo. Wannan mata ta saida yaron na ta ne a kan N10, 000.
Miss Seun Oladayo ta tabbatar da cewa ta karbi wannan kudi, ta rabu da jaririn. Matar ta bayyana wannan bayan ta shiga hannun dakarun Amotekun a jihar Ondo.
Oladayo ta ce ta saida yaron cikin na ta ne saboda tsoron za ta rasa yadda za ta dauki dawainiyarsa.
KU KARANTA: Fasto yana zargin tsohon Mai gidansa da kwanciya da Matarsa
Wannan mata ta ce tun ranar da ta sanar da mahaifin yaron cewa ta na dauke da cikinsa, ya tsere ya bar ta. Ita kuma ta ga ba ta da halin da za ta iya daukar nauyin jariri.
Bayan wannan mata ta haihu, ta datse cibiyar yaron da nufin ya mutu, ta saida shi a kan kudi N10, 000 rak ga wani Fasto, ta ce daga baya ne ta gano jaririn ya na nan da rai.
Wannan Fasto da aka saida wa jaririn ya kai maganar zuwa wajen Amotekun, daga nan aka kama ta.
Ta ce: “Da gaske ne, ina soyayya da wani mutumi mai suna Tope. Ya tambaye ni ko ina da ciki da nufin cewa zai bude mani shago, nace masa eh, ban sake ganinsa ba.”
KU KARANTA: An watsawa kishiya ruwa zafi a Kano
Fasto Olawale wanda aka fi sani da Eri Aditu, ya ce ya na karbar jaririn a buhu, ya tafi wajen jami’an Amotekun. Yanzu wannan mata ta na hannun ‘yan sanda a Yaba, Ondo.
Dazu kun samu labarin cewa an damke wani mutumi a jihar Ondo da ya ke siddabaru ya na fashi da kwanciya da matan mutane, ya ce ya kwanta da mata sama da 50.
Dakarun jami’an tsaron da aka kirkira a jihohin Kudu maso yammacin Najeriya wanda aka fi sani da Operation Amotekun ne su ka kama wannan hatsabibin mutumi.
Wannan barawon da Jami’an Amotekun suka kama ya fadi yadda ya ke kwnaciya da Mata
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng