2023: Bashir El-Rufa'i ya nuna da yiwuwar mahaifinsa da Tinubu su yiwa APC takara

2023: Bashir El-Rufa'i ya nuna da yiwuwar mahaifinsa da Tinubu su yiwa APC takara

- Tuni an fara kulle kulle dangane da takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekarar 2023

- Bashir El-Rufa'i ya nuna cewa mai yiwuwa ne mahifinsa ya yi takarar mataimaki ga Tinubu

- Lissafin takarar Tinubu a APC ya shiga tasku saboda rawar da addini ke takawa a Siyasar Nigeria

Bashir, daya daga cikin 'ya'yan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya nuna cewa mai yiwuwa ne mahaifinsa da Tinubu su rike tikitin takarar jam'iyyar APC a zaben 2023.

Tuni an fara kafa kungiyoyi da bude ofishin yakin neman takarar Tinubu a matsayin dan takarar APC a yayin da ake saka ran mulki zai koma kudu a 2023.

Takarar Tinubu ta na fuskantar tarnaki saboda rawar da addini ke takawa a siyasar Nigeria.

Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, Musulmi ne daga kudancin Nigeria, a saboda haka sai dai ya yi takara da Kirista daga arewa a matsayin mataimaki.

KARANTA: Kotu ta saurari hujjojin da PDP ta kafa akan karar da ta shigar da Yakubu Dogara

Haka jam'iyyaun siyasar a Nigeria suka saba hada 'yan takara; Musulmi daga arewa, Kirista daga kudu.

2023: Bashir El-Rufa'i ya nuna da yiwuwar mahaifinsa da Tinubu su yiwa APC takara
2023: Bashir El-Rufa'i ya nuna da yiwuwar mahaifinsa da Tinubu su yiwa APC takara
Asali: UGC

A wani sako da Bashir ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya rubuta cewa hadin kudu maso yamma da arewa maso yamma zai zama alheri ga Nigeria.

KARANTA: An kama matar dan bindigar Zamfara a cikin masu garkuwa da mutane a Kano

Bashir ya wallafa sakon ne tare da hoton Tinubu da El-Rufa'i yayin da suke cikin raha bayan sun hadu a wurin wani taro.

Sai dai, tuni masu mayar da martani suka fara yi wa Bashir raddin cewa sam ba zata yiwu a hada takarar Musulmi da Musulmi ba.

Legit.ng ta rawaito cewa Jam'iyyar PDP ta bukaci wata kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta karbar mata kujerar Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai, tare da gabatar da wasu hujjoji akansa.

Gabanin zaben shekarar 2019 ne Dogara ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Daga baya, Dogara ya sake komawa APC a 2020 bayan ya lashe zaben kujerar wakilcin mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro a majalisar wakilai ta kasa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng