Dakarun Sojojin kasa sun hallaka ‘Yan ta’adda fiye da 150 cikin makonni 3

Dakarun Sojojin kasa sun hallaka ‘Yan ta’adda fiye da 150 cikin makonni 3

- Sojojin kasa sun kashe wasu ‘Yan ta’adda 158 a watan Junairun 2021

- Ministan al’adu da yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana wannan

- Lai Mohammed ya ce an ceto mutane, kama makamai da kayan sata

A ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, Alhaji Lai Mohammed, ya ce dakarun sojojin kasa sun hallaka ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda 158.

Ministan yada labarai da al’adun Najeriya ya ce dakarun sojojin sun yi wannan namijin kokari ne daga farkon shekarar nan ta 2021 zuwa yanzu.

A cewar Mai girma Ministan, sojojin sun samu wannan nasara ne bayan an fito da sababbin dabaru, jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoto.

Alhaji Lai Mohammed ya ce daga cikin wadanda aka hallaka akwai ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram biyar, da kuma tsagerun ‘yan bindiga 118.

KU KARANTA: An cafke uba da ƴaƴan sa biyu a cikin gungun 'yan bindiga

Ministan ya kuma bayyana cewa an kama masu laifi 52, an yi nasarar karbe makamai a hannunsu.

Mohammed ya ce sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da leken asiri suna cigaba da kokarin ganin an tsare lafiya da dukiyar al’umma a fadin kasar.

Rahoton ya bayyana cewa Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin da ya zanta da manema labarai domin yin magana kan halin matsalar rashin tsaro.

Baya haka sojojin kasan sun gano ganguna 684,856 na danyen mai, da wasu litoci 1,724,000 da 500,000 da fetur da kananzir da tsageru suka sace.

KU KARANTA: An damke Mutumin da ya ke siddabaru ya na fashi da lalata da mata

Dakarun Sojojin kasa sun hallaka ‘Yan ta’adda fiye da 150 cikin makonni 3
Lai Mohammed ya na jawabi Hoto: Twitter Daga: @FMICNigeria
Asali: Twitter

A cikin nasarorin da sojojin su ka samu a jihohin Arewa, an ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su. Sojoji sun kuma tare buhuna 1,184 na takin zamani.

A makon nan ne mu ka ji cewa Rundunar 'yan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara a yakin da ta ke yi da 'yan bindiga da ta'adda a jihar Katsina.

'Yan sanda sun yi bajakolin dimbin 'yan bindiga da tarin makamansu da suka shiga hannu.

A gefe guda kuma, rundunar sojoji ta sanar da cewa ta hallaka akalla 'yan bindiga 10 tare da raunata wasu da-dama a wata arba da ka yi Batsari da Faskari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel