Gani ya kori ji: NPF ta samu gagarumar nasara akan 'yan bindigar Katsina (Hotuna)
- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta yi bajakolin wasu dumbin 'yan bindiga da tarin makamansu da aka kama
- A karshen mako ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umartar a kara tsananta yaki da 'yan ta'adda a jihar Zamfara
- Jihohin arewa da suka hada da Katsina, Sokoto, da Zamfara suna fama da hare-haren 'yan bindiga
Rundunar 'yan sandan ta samu gagarumar nasara a yaki da ta'addanci a jihar Katsina bayan ta yi bajakolin dumbin 'yan bindiga da tarin makamansu da suka shiga hannu.
A jerin wasu hotuna da Jaridar TheNation ta wallafa a shafinta na Tuwita, an ga 'yan bindiga da dama tare da dumbin miyagun makamansu yayin da aka yi holinsu a Ofishin 'yan sanda.
KARANTA: Tsohon ministan Buhari ya rasu a cibiyar killace masu cutar Korona
A ranar Talata ne rundunar soji ta sanar da cewa ta hallaka a kalla 'yan bindiga goma tare da raunata wasu masu yawa yayin wani kazamin musayar wuta da 'yan ta'addar a kananan hukumomin Batsari da Faskari a jihar Katsina.
Kazalika, rundunar sojin ta bayyana cewa ta yi rashin jami'inta guda daya yayin da wasu biyu suka samu raunuka yayin musayar wutar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
KARANTA: Farfesa Jega ya amsa tambaya akan kokarin gwamnatin Buhari tun bayan hawa mulki
Da ya ke sanar da hakan cikin wani jawabi da aka rabawa manema labarai a ranar Talata, mukaddashin darektan yada labarai a rundunar soji, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya ce sojoji sun kama mutane uku da ke taimakon 'yan bindigar.
Kazalika, Onyeuko ya sanar da cewa dakarun soji sun samu nasarar kwace makami masu dumbin yawa daga wurin 'yan bindigar.
Onyeaku ya ce dakarun rundunar atisayen Sahel Sanity ne suka samu nasarar kashe 'yan bindiga biyar yayin kowanne musayar wuta da 'yan ta'addar a kananan hukumomin Batsari da Faskari.
Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke kashe jama'a a Nigeria
A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.
Buhari ya lissafa wasu dalilai hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin baya kungiyar Boko Haram a cikin wannan shekarar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng