Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden

Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden

- Babban jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta mika rokonta na musamman ga sabon shugaban Amurka, Joe Biden

- Jam'iyyar ta bakin kakakinta, Ologbondiyan ta bukaci Shugaba Biden ya hukunta bata gari cikin shugabannin APC da jami'an gwamnati da ta ce sun aikata manyan laifuka

- PDP ta bukaci shugaban na Amurka ya duba rahotannin hukumomi kamar Amnesty International da Transparency International don ganin irin laifukan da aka aikata

Jam'iyyar PDP ta yi kira ga Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya hukunta wasu ma'aikatan gwamnati da shugabannin jam'iyyar APC kan zargin aikata rashawa, keta hakokin bil adama da wasu laifuka, The Nation ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar, jam'iyyar ta zargi wasu jami'an da bata bayyana sunansu ba da goyon bayan 'yan ta'adda tare da yi wa demokradiyya zagon kasa.

Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden
Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a barikin sojoji da ke Zaria

Don haka, jam'iyyar hamayyar ta bukaci Shugaba Biden ya dau matakin kwace kadarorin wadannan shugabannnin na APC da jami'an gwamnati da suka mallaka a Amurka.

Ta kuma bukaci shugaban na Amurka ya tabbatar basu cikin wadanda za a bawa bizan shiga kasar.

Sanarwar ta ce: "Yanzu da Shugaba Biden ya fara aiki, jam'iyyar mu na rokonsa ya duba abubuwan da suka faru musamman rahoton Department of State da kuma korafe-korafen da aka yi game da ikirarin yi wa siyasarmu zagon kasa da shugabannin APC da jami'an gwamnati suka yi.

"Muna gayyatar Shugaban Biden ya dauki mataki kan rahoton da Department of State da ke nuna keta hakkin bil adama, kisa ba tare da shari'a ba, kame ba bisa ka'ida ba, harbi da kashe masu zabe, kashe masu zanga zangan lumana kamar yadda ta faru a lokacin zanga zangar Endsars da sauran laifuka da suka yi ... wanda Amnesty International (AI) da Transparency International (TI) suka ruwaito."

KU KARANTA: Sanatan PDP ya goyi bayan Akeredolu game da fatattakar fulani daga Ondo

Har wa yau, jam'iyyar ta PDP ta bukaci Shugaba Biden ya hukunta jami'an INEC, jami'an tsaro da alkalai da lauyoyi da suka goyi bayan yi wa demokradiyya zagon kasa ta hanyar murde zabe da amfani da 'yan daba da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: