Buhari ya amince a dauki matasa masu shaidar karatu 30,000 ayyuka

Buhari ya amince a dauki matasa masu shaidar karatu 30,000 ayyuka

- Buhari ya amince da daukar matasa masu kwalin ilimin noma (agriculture) da kimiyya (sciences)

- Matasan za a ba su horon sati kan yadda ake gwajin da kusa fitar da samfurin kasa

- Babban sakataren hukumar NALDA, Paul Ikonne ne ya bayyana haka a Abuja a wani taron manema labarai

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da daukar fiye da matasa 30,000 aiki wanda za su samu horo kan harkokin noma, yadda za su duba samfurin kasa tare da gwajin samfurin kasar noma a fadin kasar nan.

Babban sakataren hukumar National Land Development Agency, NALDA, Paul Ikonne ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Buhari ya amince a dauki masu digiri 30,000 aiki
Buhari ya amince a dauki masu digiri 30,000 aiki. Hoto: NGRPresidency
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Fastocin neman takarar shugaban kasa na Wike sun bayyana a Abuja (Hotuna)

A cewar sa, matasan wanda za su samu horo kyauta na tsawon sati biyu karkashin Young Farmers Scheme.

"Za a basu horo na musamman na tsawon sati biyu kan yadda za a iya gwajin kasa don su sami ilimi akan nau'in kasa," a cewar sa.

Shugaban NALDA ya ce matasan za su kasance masu kwalin bangaren noma (agriculture) da kimiyya (sciences).

Ya ce bayan an ba su horon, za a rabawa matasan kayan gwajin kasar da na tattara nau'in kasar a karshen horon.

KU KARANTA: Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden

Ya ce manoma za su dinga biyan ₦500 ga duk gwaji guda daya, NALDA kuma zata dauki bayar da sauran kayan gwajin.

"Ba za mu iya magance matsalar abinci ba tare da sanin nau'in kasa ba, ba tare da manoma sun san irin kasar da ya kamata su yi noma da ita ba.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel