Hajiya Zeenat El-Zakzaky ba ta kamu da korona ba, Hukumar gidan gyara hali

Hajiya Zeenat El-Zakzaky ba ta kamu da korona ba, Hukumar gidan gyara hali

- Hukumar gidan yari ta kasa ta karyata rade-radin cewa uwar gidar, Sheikh Zakzaky, Haiya Zeenat ta harbu da annobar korona

- Ta ce ko daya babu wani daga cikin gidajen na jihar Kaduna da aka samu bullar wannan cutar ciki

- A cewar hukumar, suna tabbatar da an bi ka'idojin da aka shimfida na dokar

Hukumar gidan gyara hali ta Najeriya ta yi watsi labaran da ke yawo cewa matar shugaban kungiyar yan uwa Musulmai na shi’a, Zeenat Ibrahim El-Zakzaky ta kamu da korona a inda ake tsare da ita a Kaduna.

A wata sanarwa daga mai magana da yawun hukumar ta jihar Kaduna, Daniel Wadai, ya ce babu wani daga cikin gidajen jihar da aka samu bullar annobar a ciki, saboda suna tabbatar da an bi ka'idojin da aka shimfida na dokar.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki: Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa

Hajiya Zeenat El-Zakzaky ba ta kamu da korona ba, Hukumar gidan gyara hali
Hajiya Zeenat El-Zakzaky ba ta kamu da korona ba, Hukumar gidan gyara hali Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

"An ja hankalinmu kan cewa ana ta yada labarin cewa daya daga cikin mutanen da muke tsare da su a Jihar Kaduna ta kamu da korona," in ji sanarwar.

Ya kara da cewa tun a watan Maris aka dakata da karbar masu laifi cikin wadannan cibiyoyi, har sai an tabbatar da tsari mai kyau, BBC Hausa ta ruwaito.

Sanarwar ta kara da cewa "Duka gidajen da ke karkashin wannan jiha za su ci gaba da bin dokokin da aka gindaya na wannan annoba domin tabbatar da lafiyar wadanda ake tsare da su da kuma masu zuwar musu ziyara.

KU KARANTA KUMA: Prophet Okikijesu ya yi ikirarin cewa mutane na kitsa makirci kan Gwamna Wike da Yahaya Bello

A baya mun ji cewa Uwargidar shugaban kungiyar mabiya akidar Shi'a a Najeriya, Hajiya Zeenatu Zakzaky, ta kamu da cutar Coronavirus, an samu labari ranar Alhamis.

'Dan El-Zakzaky, Mohammed, ya tabbatar da halin da mahaifiyarsa ke ciki a jawabin da ya baiwa manema labarai.

Yace: "Kwanaki shida da suka gabata bayan Likitocin iyayena sun kai ziyara gudan tarin Kaduna, mahaifiyata ta fara korafin gajiya, zazzabi da kuma rashin iya shinshinan abu."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng