'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa

'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa

- 'Yan bindiga da ake zargi masu garkuwa ne sun harbi babban odita na jihar Bauchi, Abdu Aliyu da bindiga

- Hakan ya faru ne bayan sun tare motarsa a hanyarsa ta zuwa kauyensu a karamar hukumar Tafawa Balewa

- 'Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da dansa mai shekaru 25 da wani mutum mai shekaru 51 da suke cikin motar tare

'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar, Alhaji Abdu Aliyu bayan sun yi yunkurin sace shi a yammacin ranar Asabar amma hakan bai yi wu ba.

Sun sace dansa mai shekaru 25 da wani mutum mai shekaru hamsin-da-daya da suke tafiya tare a lokacin da aka kai musu harin, Channels tv ta ruwaito.

'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa
'Yan bindiga sun harbi babban odita na jihar Bauchi, sun yi awon gaba da dansa. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sanatan PDP ya goyi bayan Akeredolu game da fatattakar fulani daga Ondo

Kakakin yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakil ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce ya faru a hanyar kauyen Kardam da ke karamar hukumar Tafawa Balewa na jihar.

Wakil ya ce akwai alamun cewa yan bindigan sun rika bin motar babban oditan ne da ke hanyarsa ta zuwa kauyensu a karamar hukumar Tafawa Balewa kuma suka bude masa wuta bayan ya ki yarda su tafi da shi.

An garzaya da shi zuwa babban asibiti da ke Tafawa Balewa sannan daga bisani aka mayar da shi asibitin koyarwa ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

KU KARANTA: Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka

Rundunar 'yan sandan ta ce tuni ta fara kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da kama wadanda suka aikata laifin.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel