Sanatan PDP ya goyi bayan Akeredolu game da fatattakar fulani daga Ondo

Sanatan PDP ya goyi bayan Akeredolu game da fatattakar fulani daga Ondo

- Nicholas Tofowomo, sanatan jam'iyyar PDP mai wakiltan Ondo ta Kudu ya goyi bayan gwamna Akeredolu kan matakin korar fulani daga jiharsa

- Tofowomo ya shawarci Gwamna Akeredolu ya dauki mataki na gaba don ganin an yi doka a jihar na hana fulani zama a dazuka ba tare da rajista ba

- Sanatan ya ce kafa wannan dokar zai taimakawa gwamnatin wurin banbancewa tsakanin makiyaya na gaskiya da masu basaja suna aikata laifuka

Sanatan mai wakiltan yankin Ondo ta Kudu a Jihar Ondo, Nicholas Tofowomo, ya bayyanar goyon bayansa ga matakin da Gwamna Rotimi Akeredolu ya dauka na fatattakar fulanin da ke dazukan Jihar Ondo, Vanguard ta ruwaito.

Tofowomo, wanda sanata ne na jam’iyyar PDP, ya ce an dauki matakin ne saboda a banbacewa tsakanin masu harkalla ta gaskiya da kuma ‘yan ta’addan da ke cikin dazukan.

Sanatan PDP ya kare Akeredolu game da korar Fulani daga Oyo
Sanatan PDP ya kare Akeredolu game da korar Fulani daga Oyo. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: An fatattaki Sarkin Fulanin Oyo da iyalansa daga gidansa, an ƙone motocinsa 11

Sanatan, a cikin wani jawabi da mataimakinsa na mussamman a bangaren kafafen watsa labarai, Akinrinlola Olumide, ya shawarci gwamnan da ya dauki mataki na gaba don ganin cewa matakin ta zama doka a Jihar.

“Ina mai hada muryata da ta dukkanin mutanen kirki na cikin Jihar Ondo da kuma taya murna ga Gwamna Rotimi Akeredolu game da wannan matakin da ya dauka wanda zai kawo karshen ta’addancin da wasu gurbatattu daga cikin fulani makiyaya suke aikatawa acikin wannan Jihar mu ta Ondo.”

“A yayin da nake bayyana goyon baya ta dari bisa dari akan wannan matakin da gwamnan ya dauka na korar ‘yan ta’adda daga dazukan mu tare da yin rajista ga makiyaya da manoma masu kasuwanci ta gaskiya acikin Jihar Ondo, ina rokon shi ya dauki matakin ganin cewa hakan ya zama doka.”

KU KARANTA: Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka

“Ya kamata ya tsara doka ya mika zuwa ga majalisar dokoki ta Jihar wanda za ta kawo karshen fashi da makami, garkuwa da mutane, wanda wasu gurbatattu daga cikin fulani ke shiryawa, inda suke badda kama a matsayin makiyaya.”

“Da wannan ne za’a iya fayyacewa tsakanin ‘yan ta’adda da kuma masu harkalla ta gaskiya a wannan Jihar ta Ondo. Dan fashi ne kadai zai goyi bayan dan fashi, hakazalika mai garkuwa da mutane kadai zai goyi bayan mai garkuwa da mutane.”

Tofowomo ya kara da cewa “Ina tare da gwamna a wannan mataki da ya dauka. Kuma ina shawartan dukkan Fulani na gaskiya dasu bi umurnin gwamna na barin dazukan garin, tare da bin hanyoyin da ya dace na yin rajista.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel