Hare-hare akan makiyaya: Miyetti Allah ta bawa gwamnatin tarayya wata shawara a fusace
- Har yanzu cacar baki da musayar yawu bata kare ba akan batun korar makiyayaya daga wasu jihohin kudu
- Gwamnan Ondo ya umarci makiyaya su tattara kayansu su fice daga jiharsa bisa zarginsu da aikata miyagun laifuka
- Kazalika, wasu 'yan kabilar Yoruba sun kone gidan sarkin Fulanin jihar Oyo bayan umarnin da gwamnan Ondo ya bayar
Kungiyar Miyetti Allah Kautal Haure ta yi kira tare da bawa gwamnatin tarayya shawarci akan ta amince da bukatar raba Nigeria, kowanne yanki ya kama gabansa.
Sakataren kungiyar, Saleh Alhassan, ne ya sanar da hakan yayin wata tattaunawarsa da jaridar Punch a ranar Asabar.
A cewar Alhassan, ana nunawa kabilar Fulani kyama a kasa, a saboda haka zai fi kyautuwa a raba kasar domin su samu tsaro.
DUBA WANNAN: Farfesa Wole Soyinka: Na yafewa Amurkawan da suka zabi Trump, yanzu zan iya komawa Amurka
An dade ana kiraye-kirayen neman a sake fasalin mulki da tsara gudanar da gwamnatin Nigeria. Shugabanni da jagororin al'ummar yankin kudu sun kafe akan cewa hakan ne kadai zai kawo cigaba da zaman lafiya a kasa.
DUBA WANNAN: 2023: Ba wata Biafra; Dattijo daga kabilar Igbo ya bayyana neman takarar shugaban kasa
Sakataren ya bayyana cewa kuskure ne a yi wa wata Kabila hukunci saboda laifukan wasu tsirarun cikinta tare da bayyana cewa basa goyon bayan ta'addanci ko aikata kowanne irin laifi.
Legit.ng ta rawaito cewa sanatan mai wakiltan yankin Ondo ta Kudu a Jihar Ondo, Nicholas Tofowomo, ya bayyanar goyon bayansa ga matakin da Gwamna Rotimi Akeredolu ya dauka na fatattakar fulanin da ke dazukan Jihar Ondo.
Tofowomo, wanda sanata ne na jam’iyyar PDP, ya ce an dauki matakin ne saboda a banbacewa tsakanin masu harkalla ta gaskiya da kuma ‘yan ta’addan da ke cikin dazukan.
Tofowomo, wanda sanata ne na jam’iyyar PDP, ya ce an dauki matakin ne saboda a banbacewa tsakanin masu harkalla ta gaskiya da kuma ‘yan ta’addan da ke cikin dazukan.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng