Prophet Okikijesu ya yi ikirarin cewa mutane na kitsa makirci kan Gwamna Wike da Yahaya Bello

Prophet Okikijesu ya yi ikirarin cewa mutane na kitsa makirci kan Gwamna Wike da Yahaya Bello

- Babban faston Najeriya, Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi hasashen cewa wasu gwamnoni na cikin hatsari

- Okikijesu ya ce wasu mutane ne ke shirya munakisa domin lalata gwamnatinsu

- Ya kuma kalubalance su da su dage sosai da addu'a domin dakile wannan yunkuri na mutanen

Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi gargadin cewa akwai wani makiri da ake yi don lalata gwamnatin gwamnonin Najeriya guda biyar.

Babban faston a cikin wata sanarwa ya yi ikirarin cewa Allah ya bayyana masa cewa wasu mutane sun hade don tarwatsa mulkin gwamnonin da ake magana a kansu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin tarayya ta dage ranar dawowarta zama

Prophet Okikijesu ya yi ikirarin cewa mutane na kitsa makirci kan Gwamna Wike da Yahaya Bello
Prophet Okikijesu ya yi ikirarin cewa mutane na kitsa makirci kan Gwamna Wike da Yahaya Bello @PremiumTimesng
Asali: Twitter

A cewar Okikijesu, gwamnonin da abun ya shafa sun hada da:

1. Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers

2. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi

3. Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo

4. Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo

5. Gwamna Abubakar Bello na jihar Niger

Faston ya ce wadannan gwamnoni da aka ambata su dage da addu’a da sanya idanu sosai domin dakile makircin da ake kullawa a kansu.

A cewar faston, wadanda ke shirin a kan gwamnonin sun jajirce domin aiwatar da mummunan nufin nasu.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki: Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa

Ya yi ikirarin cewa a yanzu haka makiran na daukar matakai don cimma wannan manufa nasu tsakanin Janairu da Maris 2021.

A baya, Apostle Paul Okikijesu na cocin Christ Apostolic Miracle Ministry ya yi ikirarin cewa Allah ya bayyana masa cewa wani gwamnan Najeriya zai mutu a 2021.

Okikijesu wanda yayi ikirarin a wani wahayi da ya saki na sabuwar shekaara ya ce mutuwar gwamnan namiji zai ba mace damar zama gwamna.

Sai dai malamin bai bayyana jihar Najeriya da hasashensa zai fada a kai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel