Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin tarayya ta dage ranar dawowarta zama
- Majalisar dokokin tarayya ba za ta dawo zama a ranar da aka shirya dawowarta ba
- Hakan ya kasance ne saboda wani atisaye da jam'iyyar All Progressives Congress mai mulki za tayi wanda ke bukatar mambobin jam'iyyar su shiga ciki
- Wata sanarwa daga shugabanin majalisar dokokin kasar ta ce a yanzu dukkanin majalisun dokokin za su dawo zama a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu
Majalisar dokokin tarayya ta dage ranar dawowarta zama har zuwa ranar Talata, 9 ga watan Fabrairun 2021.
Magatakardan majalisar dokokin tarayyar, Ojo Amos ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gani a Abuja a ranar Asabar, 23 ga watan Janairu.
KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki: Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa
Amos ya ce an dage zaben ne domin baiwa ‘yan majalisar, wadanda suke mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), damar yin rajistar zama mambobin jam’iyyar da kuma sake ragin da aka fara wanda zai fara a ranar Litinin, 25 ga watan Janairu.
Wasu ‘yan Najeriya sun yi mayar da martani game da sanarwar da shugabannin Majalisar suka yi ta kafofin sada zumunta.
A wani labarin, Hashim Ubale Yusufu ya yi wata hira da jaridar Daily Trust, ya tabbatar da cewa an yi yarjejeniya cewa mulki zai koma yankin kudu a shekarar 2023.
Mun tsakuro maku wasu daga cikin bayanan da aka samu a hirar da aka yi da ‘dan siyasar.
KU KARANTA KUMA: Karon farko a shekarar 2021: Babu wanda ya kamu da cutar COVID-19 a Lagos
Da aka tambayi Ubale Yusufu a kan wanda za a mika wa mulki sai ya ce: “Ba alkawari aka yi a rubuce ba. Kusan wani abu ne mai kamar yarjejeniya.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng