Karon farko a shekarar 2021: Babu wanda ya kamu da cutar COVID-19 a Lagos

Karon farko a shekarar 2021: Babu wanda ya kamu da cutar COVID-19 a Lagos

- Jihar Lagas bata samu ko mutum daya da ya kamu da cutar korona ba a ranar Juma'a, 22 ga watan Janairu

- Wannan shine karo na farko da ba a samu wanda ya harbu ba a jihar cikin shekarar 2021

- Har yanzu dai jihar Lagas ce cibiyar annobar a Najeriya

Karo na farko a 2021, Jihar Legas ba ta sami wani sabon rahoton COVID-19 ko mutuwa daga cutar ba a ranar Juma’a, 22 ga watan Janairu.

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ce ta bayyana hakan a cikin sanarwa da ta saki na yau da kullun game da cutar.

Ba a bayar da dalili kan halin da ake ciki a Legas ba a ranar Juma’a.

Sai dai, a baya, wasu jihohin da galibi suke samun sabbin wadanda suka harbu a rahoton yau da kullun, kamar su Kano, ba su kan samu sabbin mutane dasuka harbu saboda rashin gudanar da gwaji a wadannan rana,musamman saboda zanga-zangar ma’aikata.

Karon farko a shekarar 2021: Babu wanda ya kamu da cutar COVID-19 a Lagos
Karon farko a shekarar 2021: Babu wanda ya kamu da cutar COVID-19 a Lagos Hoto: National Accord Newspaper
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen manyan attajiran Africa guda 10, Dangote, Adenuga da Rabiu na ciki

Kuma har yanzu Lagas ita ce cibiyar cutar a Najeriya.

Yayinda ba a samu sabbin wadanda suka kamu ba a Lagas, Najeriya ta samu sabbin mutane 1,483 da suka harbu a ranar Juma’a, inda Karin mutum biyar suka mutu sakamakon cutar yayinda ake kokarin kawo rukunin farko na rigakafin cutar cikin kasar.

Hakan na zuwa ne kimanin sa’o’i 24 bayan Najeriya ta samu mafi yawan wadanda suka kamu a ranar Alhamis.

Alkalumman da NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa an samu karin mutum 1,483 da suka kamu da annobar korona a kasar.

Sannan jihar Kaduna ce kan gaba inda mutum 545 suka kamu da korona a jihar. Haka kuma a Abuja mutum 235 suka kamu da cutar yayin da kuma a jihar Filato 127 suka kamu.

KU KARANTA KUMA: Bayan kamuwa da corona: IMN na so a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa

A Kano mutum 46 suka kamu, a Gombe mutum 30. A Sokoto mutum 12 a Zamfara kuma mutum 10.

A wani labarin, Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa amfanin barin yara su koma makaranta ya rinjayi tsoron kamuwa da cutar Korona.

Ihekweazu ya bayyana hakan a taron kungiyar likitocin yaran Najeriya watau (PAN) ranar Juma'a a jihar Legas, The Cable ta ruwaito.

Ihekweazu ya ce lallai ya yi na'am da shawaran bude makarantu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng