COVID-19: NCDC ta rahoto karin mutum 1,964 sun harbu da cutar

COVID-19: NCDC ta rahoto karin mutum 1,964 sun harbu da cutar

- Ga yan Najeriya da suka ki yarda akwai annobar korona a Najeriya, shakka babu alkaluman wadanda suka kamu a ranar Alhamis, 21 ga watan Janairu zai sauya tunaninsu

- Kasar ta samu mafi yawan mutanen da suka harbu a rahoton yau da kullun da take saki tun bayan bayyanar annobar a cikinta

- NCDC ta bayyana cewa Karin mutum 1,964 sun harbu a daren ranar Alhamis

Tun bayan barkewar annobar korona a Najeriya a farkon shekarar 2020, yawan wadanda suka kamu da cutar a ranar Juma’a, 22 ga watan Janairu, (1,964) shine mafi yawa da aka taba samu na adadin wadanda ke kamuwa da cutar a kulla-yaumin.

Bugu da kari, hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) a wani wallafa da tayi a shafin Twitter ta bayyana cewa kasar ta rasa mutum bakwai sakamakon cutar cikin kwana daya kacal.

A halin yanzu dai kididdigar masu cutar a Najeriya ita ce 116,655 sannan mutane 93,646 sun warke inda kuma mutane 1,485 suka mutu.

COVID-19: NCDC ta rahoto karin mutum 1,964 sun harbu da cutar
COVID-19: NCDC ta rahoto karin mutum 1,964 sun harbu da cutar Hoto: @NCDCgov
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Kuyi koyi da Gumi wajen yi wa yan bindiga da'awah, Matawalle ga malaman Zamfara

Har yanzu Lagas ce cibiyar annobar a kasar, inda take da sabbin mutane 824 da suka kamu yayinda babbar birnin tarayya ta biyo baya da mutanne 246 da suka harbu.

Sauran jihohin da ke da karancin wadanda suka harbu sune kamar haka:

Plateau (166), Kaduna (128), Ogun (76), Nasarawa (74), Anambra (69), Edo (50), Rivers (45), Ondo (44), Niger (40), Oyo (38), Adamawa (35), Kano (31), Akwa Ibom (27), Gombe (19), Kwara (13), Ekiti (12), Delta (6), Kebbi (6), Bauchi (5), Ebonyi (4), Osun (3), da Zamfara (1).

KU KARANTA KUMA: Kungiyar gwamnoni tayi martani yayinda Yahaya Bello yace kashe mutane ake so ayi da rigakafin korona

A geefe gud, gwamnatin Babban Birnin Tarayya (FCTA) a ranar Alhamis ta sanar da mazauna cewa akwai 'yan damfara wadanda ake zargin suna zagayawa don karbar kudade daga masu shirya taro da sauran wurare a garin da sunan masu aiwatar da binciken COVID-19.

Shugaban Kafafen yada labarai da wayar da kai na rundunar tsaro kan COVID-19 ta FCT, Kwamared Ikharo Attah wanda ya yarda da faruwar irin wadannan munanan rahotanni, ya gargadi jama'a da su yi taka tsantsan.

Yayin da yake karyata jita-jitar da ake yadawa cewa mambobin rundunarsa na da hannu a aikata laifin, ya kuma bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta FCT ta fara farautar masu aikata laifin, The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel