Kasafin kudi: Za mu karbo bashin N4.8t a shekarar 2021 inji Shugaba Buhari

Kasafin kudi: Za mu karbo bashin N4.8t a shekarar 2021 inji Shugaba Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya kai wa Majalisa kundin kasafin kudin 2021

- Gwamnatin Tarayya za ta karbo bashi domin cike gibin da aka samu a kasafin

- Bayan haka za a biya sama da Naira Tiriliyan 3.1 wajen biyan tsofaffin bashi

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kundin kasafin kudin shekarar 2021 a gaban ‘yan majalisa domin ayi maza a amince da shi a matsayin doka.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto cewa shugaban kasar ya bayyana gaban ‘yan majalisa ne tare da mataimakinsa, da wasu ministoci da hadimansa.

Shugaban Najeriyar ya bayyana cewa abin da ake hangen cewa gwamnatin tarayya za ta iya samu a matsayin kudin shiga a 2021, ba zai wuce Naira tiriliyan 7.86.

KU KARANTA: Buhari ya na gabatar da kasafin shekarar 2021 a Majalisa

Hakan ya na nufin an bar gwamnatin tarayya da gibin sama da Naira tiriliyan 5.2, ma’ana sai an ci bashin 3.4% na jimillar tattalin arzikin Najeriya a shekarar.

Bayan kudin shiga da za a samu daga albarkatun kasa irinsu danyen mai da Najeriya ta dogara da shi, gwamnati za ta samu gudumuwar Naira biliyan 354.85.

Daga bangaren mai, gwamnatin Najeriya na harin Naira tiriliyan 2.01, sai kuma kusan Naira tiriliyan 1.5 daga sauran albarkatun da kasar ta dogara da su.

A shekarar 2021, ma’aikatun gwamnatin tarayya za su dage da neman kudin shiga da kansu.

KU KARANTA: Za mu hukunta masu daukar aiki ba tare da bin ka'ida ba - Buhari

Kasafin kudi: Za mu karbo bashin N4.8 a shekarar 2021 inji Shugaba Buhari
Shugaba Buhari a gaban 'Yan Majalisa Hoto: Twitter/BashirAhmaad
Asali: Facebook

Kamar yadda shugaban kasa ya bayyana a jiya, ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya 60 ake sa ran za su tatsowa gwamnati kudin shiga a shekarar badi.

Gibin da za a samu a kasafin kudin na badi zai fito ne daga bashin Naira tiriliyan 4.8 da za a ci. Za a kuma saida kadarorin Naira Biliyan 205.15 a shekarar 2021.

A shekara mai zuwa, gwamnatin Najeriya za ta biya bashin Naira tiriliyan 3.12, akasin abin da ta kashe a 2020 na Naira tiriliyan 2.1 wajen biyan bashin da ta ci.

Dazu mun kawo maku takaitaccen bayani game da bashi, albashi da kudin ayyukan da aka ware a kasafin kudin 2021, inda Najeriya ta ke shirin batar da N13.08tr.

Gwamnatin Najeriya za ta kashe kaso mai tsoka waje biyan bashi da albashin ma’aikata a badi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel