Amaechi ya caccaki Jigon PDP, ya ce har Gwamnatin Jonathan ta karbo aron kudi daga Sin

Amaechi ya caccaki Jigon PDP, ya ce har Gwamnatin Jonathan ta karbo aron kudi daga Sin

- Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi, ya kare Gwamnatin Shugaba Buhari

- Ana ta surutu a game da bashin Dala miliyan 500 da su ka karbo daga kasar Sin

- Amaechi ya ce Gwamnatin da ta shude ma ta karbo irin wannan bashi daga waje

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba a kan ta ne aka fara karbo bashin kudi a Najeriya ba.

Gwamnatin ta kare kanta ne ta bakin Rt. Hon. Rotimi C. Amaechi.

Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce ana kokarin karkatar da hankalin gwamnati mai-ci da suka kan cin bashi domin Goodluck Jonathan ma ya ci bashi daga waje.

Mai girma Rotimi Amaechi ya ce abin da ya kamata mutane su rika tattaunawa a kai shi ne yadda gwamnatin Najeriya za ta biya wannan bashi da ta karbo daga kasar Sin.

Amaechi ya yi wannan bayani ne lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, inda ya maida martani game da kalaman wani ‘dan adawa.

KU KARANTA: Abin da ya sa na shiga siyasa tun farko inji Rotimi Amaechi.

Amaechi ya caccaki Jigon PDP, ya ce Gwamnatin Jonathan ta karbo aron kudi daga Sin
Amaechi ya ce ba zai yi murabus ba
Asali: Twitter

Kafin nan, Katch Ononuju, wani jagoron jam’iyyar PDP, ya shiga gidan talabijin ya na cewa ya kamata Ministan ya ajiye kujerarsa a dalilin yawon bashin da ya ke karbowa.

Ministan ya ce: “Akwai wani Bawan Allah da ya je AIT ya na cewa in yi murabus. Murabus saboda mene? Za ka ce wadannan ayyyuka (da aka yi da bashin nan) ba su nan ne?

"Babu titin dogon Kaduna zuwa Abuja?" Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ke tambaya.

A cewar Rotimi Amaechi, gwamnatin PDP wanda Dr. Goodluck Jonathan ya jagoranta tsakanin 2010 zuwa 2015 ne ta ci bashin yin gagarumin aikin jirgin Kaduna zuwa Abuja.

“Gwamnatin Goodluck Jonathan ce wanda ta karbo bashin nan (da Ononuju ya ke magana a kai), a dalilin haka mu ka sa wa tashar jirgin Agbor sunan (tsohon shugaban kasar)."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel