Sokoto: 'Yan jari bola sun mamaye kasuwar Sokoto jim kadan bayan lafawar gobarar kasuwa

Sokoto: 'Yan jari bola sun mamaye kasuwar Sokoto jim kadan bayan lafawar gobarar kasuwa

- Matasa 'yan jari bola sun mamaye babbar kasuwar garin Sokoto bayan lafawar gobarar sa'a fiye da goma

- Wasu daga cikin masu shaguna a kasuwar ne suka kira 'yan jari bolar domin sayar musu sauran kayan da wuta ta babbake

- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kai ziyarar jaje zuwa jihar Sokoto tare da bayar da tallafin miliyan N500

Kwana daya kacal bayan lafawar gobarar da ta tafka barna a babbar kasuwa Sokoto, 'yan jari bola sun mamaye kasuwar domin tsintar duk wani abu da wuta ta lalata.

Wakilin Daily Trust da ya ziyarci ksuwar ya tabbatar da cewa ya ga daruruwan 'yan jari bola suna tsintar kayayyaki suna zubawa a cikin buhunhunansu da ke cikin amalanke masu kafa biyu.

Daily Trust ta rawaito cewa wasu daga cikin masu shagunan da suka kone ne suka kira 'yan jari bolar domin sayar musu da sauran kayayyaki da wuta ta kammala cinyewa bayan gobarar sa'a goma.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Sokoto: 'Yan jari bola sun mamaye kasuwar Sokoto jim kadan bayan lafawar gobarar kasuwa
Sokoto: 'Yan jari bola sun mamaye kasuwar Sokoto jim kadan bayan lafawar gobarar kasuwa
Asali: Twitter

KARANTA: Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Teti, shekara fiye da 2,500 baya

Duk da har yanzu babu wata sanarwa a hukumance dangane da sababin tashin gobarar, wasu majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa gobarar ta samo asali ne daga injin janeraton samar da wutar lantarki.

Tuni shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da sauran shugabanni da jagororin al'umma suka fara aika sakonninsu na jaje zuwa ga gwamnati da jama'ar jihar Sokoto.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kai ziyara jihar Sokoto don jajantawa takwaransa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, bisa mummunar gobarar kasuwar da ta faru ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Yayin ziyarar, gwamna Wike ya bawa gwamnatin jihar Sokoto gudunmuwar milyan dari biyar (N500,000,000) domin sake gina kasuwar.

Hakazalika, Wike ya kai ziyara fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubuakar Sa'ad.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel