Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane

Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane

- A ranar Laraba gwamnatin jihar Kano ta umarci a rushe wani gida da ake zargin ana adana wadanda aka yi garkuwa dasu

- Gidan yana Jaba quarters dake karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, jama'a sun taru sun yi makil lokacin da ake rusau

- 'Yan sanda sun samu nasarar kama masu garkuwa da mutanen, ciki har da wata bazawara wacce aka kashe mijinta yaje satar shanu

A ranar Laraba, gwamnatin jihar Kano ta fada wani gida wanda ake zargin masu garkuwa da mutane suna adana mutane idan sun sato su.

Premium Times ta ruwaito yadda a ranar Laraba 'yan sanda suka kwashe wasu masu garkuwa da mutane, ciki har da wata bazawara.

Ma'aikatan KNUPDA da jami'an tsaro sun kula da yadda bulldozer ta kwashe ginin tsaf dake Jaba a karamar hukumar Ungogo dake Kano.

Jama'a da dama sun taru suna ganin yadda aka kwashe ginin.

KU KARANTA: Dattawan arewa sun bukaci makiyaya da su yi watsi da umarnin Akeredolu

Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane
Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Jami'an sun ce za su tura soko ga mutanen gari da su cigaba da kulawa da anguwanninsu da kuma gidajensu ga masu bayar da haya.

Wacce ake zargin, Maryam Mohammed, mai shekaru 23 ta sanar da manema labarai yadda ta sace tsohon saurayinta wanda ya yaudareta ya ki aurenta bayan sun kwashi shekaru suna soyayya.

A cewarta, kawunta Hamza Dogo ne ya koya mata wannan harkar, bayan ta rabu da tsohon saurayinta.

Ta bayyana yadda kawunta yasa ta yaudari saurayinta ta kai shi suka boye shi, suka bukaci N5,000,000 kafin su sake shi. Sai da aka tura musu N800,000 sannan suka sake shi. Kuma sun adana shi ne a Jaba quarters.

Kamar yadda 'yan sanda suka gano, Maryam tsohuwar matar Sani Isma'il ne na karamar hukumar Bidda dake jihar Neja. Isma'il shu'umin barawon shanu ne, wanda aka kashe a kauyen Butsa dake karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Majalisa ba za ta yaki Buhari ba saboda son farantawa wasu rai, Lawan

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Daily Trust ta wallafa.

An kama daya daga cikin ma'aikatan tsaro na jami'ar mai suna Aliyu Abubakar sakamakon bai wa masu garkuwa da mutanen tallafi a dukkan lokutan da suke sace jama'a a jami'ar.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, CP Frank Mba, ya sanar da damke wani Malam Jafaru da ke samar da asiri ga masu garkuwa da mutanen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel