Dattawan arewa sun bukaci makiyaya da su yi watsi da umarnin Akeredolu

Dattawan arewa sun bukaci makiyaya da su yi watsi da umarnin Akeredolu

- Kungiyar dattawan arewa ta hassala da kalaman gwamnan jihar Ondo, wanda ya umarci Fulanin jiharsa da su bar dajikan jihar cikin kwana 7

- Kakakin kungiyar dattawan, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce lallai gwamnan ya janye zancensa cikin gaggawa saboda hakan tozarci ne

- Baba Ahmed ya ce Fulani sun dade a cikin jihar Ondo kuma sun tashi cikin mako, rashin tausayi ne da rashin imani

Shugaban kungiyar dattawan arewa ya dakatar da makiyayan jihar Ondo daga barin mahallinsu kuma kada su yarda a dinga siffantasu da 'yan ta'adda kuma masu laifi.

A wata takarda ta ranar Laraba, Hakeem Baba-Ahmed, kakakin kungiyar ya umarci Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, da ya ajiye batun bai wa makiyayan jiharsa lokaci na su tattara ya nasu ya nasu su bar dajikan dake jiharsa.

Ya bayyana gwamnan a matsayin wanda ba ya taimako kuma macuci, The Cable ta ruwaito.

Dattawan arewa sun bukaci makiyaya da su yi watsi da umarnin Akeredolu
Dattawan arewa sun bukaci makiyaya da su yi watsi da umarnin Akeredolu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

A ranar Litinin, Akeredolu ya bai wa makiyaya kwana 7 da su tattara duk abubuwan da suka mallaka su bar dajikan dake jiharsa, bayan fara hauhawar matsalolin tsaro.

Gwamnan ya ce makiyaya sun fara mayar da dajikan jiharsa wurin boye wadanda suke garkuwa dasu, don haka ba zai lamunta ba.

Sai dai Baba-Ahmed ya ce Fulani ba za su amince da irin wannan zalunci da cin zarafin ba. Ya bukaci gwamnan ya ware 'yan ta'adda sai ya tozarta su yadda ya ga dama.

"NGF ta yi mamakin kalaman gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, SAN, wanda ya ke bukatar Fulani su bar inda suke a jiharsa, mutanen da suka shude shekaru suna zama a wurin," cewar Baba-Ahmed.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Majalisa ba za ta yaki Buhari ba saboda son farantawa wasu rai, Lawan

A wani labari na daban, Jam'iyyar APC mai mulki ta musanta ikirarin jam'iyyar adawa ta PDP na cewa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Dogara, wanda aka zaba domin wakilci a majalisar wakilai a zaben da ya gabata karkashin jam'iyyar PDP, ya koma jam'iyyar APC a shekarar da ta gabata.

Wannan musantawar ta jam'iyyar APC na dauke ne a wata takarda da ta mika gaban kotu wacce take martani ga PDP a gaban kotun bayan sun bukaci a kwace kujerar Dogaran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel