Miyetti Allah ya jinjinawa Fadar Shugaban kasa, ta ce makiyaya ba bata gari bane

Miyetti Allah ya jinjinawa Fadar Shugaban kasa, ta ce makiyaya ba bata gari bane

- Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta yaba wa Fadar Shugaban Kasa saboda taka wa gwamnan Ondo birki kan korar makiyaya daga jiharsa

- Kungiyar ta ce Fadar Shugaban Kasar ta yi dai-dai kuma abinda ta fada shine abinda ke cikin kudin tsarin mulki

- MACBAN ta umurci mambobinta su cigaba da zama inda suke domin biyayya da umurnin shugaban kasar da kuma kudin tsarin mulki

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, MACBAN, ta yabawa Fadar Shugaban Kasa saboda saka baki cikin batun umurnin da gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akerelodu ya bada na korar makiyaya daga dazukan da ke jiharsa.

Sakataren kungiyar na kasa, Usman Baba-Ngelzerma ya shaidawa The Punch a ranar Laraba cewa Fadar Shugaban Kasar ta fadi gaskiya a yayin da ta ce makiyayyan su cigaba da zamansu a jihar.

Miyetti Allah ya jinjinawa Fadar Shugaban kasa, ta ce makiyaya ba bata gari bane
Miyetti Allah ya jinjinawa Fadar Shugaban kasa, ta ce makiyaya ba bata gari bane. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wanda ya na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

Da ya ke mayar da martani ya ce, "Don me zan saba umurnin shugaban kasa? Yana magana ne a madadin kasa baki daya. Yana jadadda abinda kundin tsarin mulki ne ya fada, illa iyaka. Abinda Fadar Shugaban Kasa ta fadi shine abinda ya dace. Fadar Shugaban Kasar ta jadadda abinda kundin tsarin mulki ya ce."

Baba-Ngelzerma ya ce kawo yanzu kungiyar ta makiyaya ba ta samu wani umurni a hukumance da ke neman su fice daga jihar ba.

Ya ce a halin yanzu, makiyayan za su cigaba da zama a inda suke, ya kara da cewa suna zaune lafiya da mutanen garuruwan.

KU KARANTA: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

A ranar Litinin ne Akeredolu ya fitar da sanarwar cewa makiyaya su fice daga dazukan da ke jihar saboda karuwar garkuwa da mutane a jihar.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164