Yan sanda sun kama mambobin hatsabibiyar kungiyar nan ta yan Shilla su 3 a Yola

Yan sanda sun kama mambobin hatsabibiyar kungiyar nan ta yan Shilla su 3 a Yola

- Jami'an yan sanda a Yola sun kama wasu mambobin kungiyar yan Shilla su uku

- An samo keken adaidaita sahu, wukake da adduna a hannun yan ta'addan

- Kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da kamun nasu

Rundunar yan sanda a garin Yola, babbar birnin jihar Adamawa ta tabbatar da kama mutum uku daga cikin mambobin hatsabibiyar kungiyar nan da aka fi sani da “Yan Shilla”.

DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya kasance kakakin rundunar yan sanda a jihar ne ya tabbatar da kamun nasu a wata sanarwa.

Nguroje ya bayyana cewa wadanda aka kama suna a tsakanin shekaru 18 da 35 kuma sun dade sun addaban mutane da mugan makamai a wasu yankuna na karamar hukumar Yola ta arewa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yan sanda sun kama mambobin hatsabibiyar kungiyar nan ta yan Shilla su 3 a Yola
Yan sanda sun kama mambobin hatsabibiyar kungiyar nan ta yan Shilla su 3 a Yola Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa kungiyar yan ta’addan kan badda kamanni a matsayin masu tuka adaidaita sahu wajen yiwa fasinjoji da basu ji ba basu gani ba fashi.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar gwamnoni tayi martani yayinda Yahaya Bello yace kashe mutane ake so ayi da rigakafin korona

Ya ce a ranar 20 ga watan Janairu yan sanda sun samu bayanai game da kai kawon yan kungiyar a mabuyarsa da ke garin Ngurore.

“Nan take sai rundunar yan sandan ta aika jami’anta zuwa yankin sannan suka yi nasarar kama yan Shillan su uku,” in ji shi.

Nguroje ya lissafa kayayyakin da aka kwato daga hannun miyagun da suka hada da keken adaidaita sahu daya, wukake da adduna.

Ya ce ana bincikensu kan hada kai wajen ta’addanci da fashi da makami sannan za a mika su kotu da zaran an kammala bincike.

Ya yaba ma mutane kan yadda suke ba yan sanda hadin kai, musamman ta banaren bayar da bayanai abun dogaro.

KU KARANTA KUMA: Katin dan kasa: FG ta sanar da ranar rijistan NIN na karshe da toshe layukan waya

A wani labarin, rundunar yan sandan Jihar Kano a ranar Laraba ta cafke wasu masu garkuwa da mutane su hudu cikin su har da mace ƴar shekara 23, Maryam Mohammed, Daily Trust ta ruwaito.

Ta shaida cewa aikin ta na farko a matsayin mai garkuwa da mutane ya fara ta kan tsohon saurayin ta wanda yaki auren ta bayan shafe shekaru suna soyayya.

Maryam Mohammed, wanda aka fi sani da Hajiya, an kama ta a ranar Talatar da ta gabata tare da wasu mutane uku yan tawagar ta a unguwar Jaba, karamar hukumar Ungogo da ke Jihar Kano, lokacin da suke tattaunawa da iyalan daya daga cikin wanda suka sace akan kudin fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng