Katin dan kasa: FG ta sanar da ranar rijistan NIN na karshe da toshe layukan waya

Katin dan kasa: FG ta sanar da ranar rijistan NIN na karshe da toshe layukan waya

- Hukumar NCC ta ce babu ja da baya kan wa’adin ranar 9 ga watan Fabrairu don alakanta NIN da layukan SIM

- Sai dai kuma hukumar ta nuna gamsuwa kan yadda yan Najeriya ke amsa lamarin

- A cewar NCC, masu amfani da layukan waya sun karbi lambobinsu na NIN guda miliyan 47.8

Yayinda fargaba ya cika kasar kan hade layukan waya da lambobin shaidar zama yan kasa (NIN), gwamnatin tarayya a ranar Talata, 19 ga watan Janairu, ta ce tana nan kan bakarta na wa’adin 9 ga watan Fabrairu.

Da take magana kan ci gaban, hukumar kula da sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce an fada ma kamfanonin sadarwa da su rufe layukan da ba a yiwa NIN ba bayan ranar karshe.

Legit.ng ta lura cewa yan Najeriya na ta rokon gwamnati kan ta kara wa’adin da ta bayar, inda suka yi nuni ga yawan mutanen da ke kasar.

Katin dan kasa: FG ta sanar da ranar rijistan NIN na karshe da toshe layukan waya
Katin dan kasa: FG ta sanar da ranar rijistan NIN na karshe da toshe layukan waya Hoto: @NCCgov
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Bauchi ya gana da Atiku a Dubai yayinda aka fara tattauna batun 2023

Amma NCC, ta kwamitin TIC ta ce babu gudu ba ja da baya a hukuncinta.

Sai dai ta nuna gamsuwa a kan yadda yan Najeriya suka ba abun muhimmanci yayinda masu amfani da layuka 47.8 miliyan suka gabatar da lambobin NIN dinsu, jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Wani bangare na jawabin da daraktan harkokin jama’a na NCC, Ikevhukwu Adinde ya saki ya zo kamar haka:

“Zuwa yanzu, masu amfani da wayoyi sun karbi jumular NIN miliyan 47.8. Inda mutum daya ke da akalla layuka 3 zuwa 4.

“Hakan na nufin za a sada wasu karin miliyoyin layukan waya kafin ranar karshe da aka bayar a watan Fabrairun 2021.”

KU KARANTA KUMA: Buhari ya jajantawa iyalan tsohon ministan wasanni, Bala Ka’oje

A wani labarin kuma, mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo (SAN) ya ce hangen nesan gwamnatin Buhari na fitar da akalla ‘yan Najeriya miliyan 20 daga kangin talauci a cikin shekaru biyu masu zuwa yanzu ya kusa.

Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 19 ga watan Janairu a Abuja yayin fara shirin fara hada hadar kudade da gwamnatin tarayya ta fara.

Wata sanarwa daga Laolu Akande, mai magana da yawun mataimakin shugaban, wanda Legit.ng ta gani ta nakalto Osinbajo yana cewa shirin zai taimakawa gwamnatin tarayya wajen cimma burinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel