Rashin tsaro: 'Yan arewa ba su jin daɗin mulkinka, Bafarawa ga Buhari

Rashin tsaro: 'Yan arewa ba su jin daɗin mulkinka, Bafarawa ga Buhari

- Bafarawa ya bayyana yadda rashin tsaro ke damun yan arewa ranar Laraba a Abuja

- Ya bukaci gwamnati ta maida hankali kan matsalar tsaro fiye da annobar COVID-19

- Ya roki gwamnati ta karkatar da akalar biliyan 400 na rigakafin COVID-19 don magance rashin tsaro

Tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Attihiru Dalhatu Bafarawa, ya ce yan arewa da duk yan kasa ba sa jin dadin halin rashin tsaro da kasar ke ciki, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da hankali ga matsalar tsaro fiye da COVID-19.

Bafarawa ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ga yan kasa ranar Laraba a Abuja.

Rashin tsaro: 'Yan arewa ba su jin dadin mulkinka, Bafarawa ga Buhari
Rashin tsaro: 'Yan arewa ba su jin dadin mulkinka, Bafarawa ga Buhari
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

A cewar sa, rashin tsaro ya kashe dubban rayuka fiye da yadda annobar COVID-19 ta yi.

Ya kuma bayyana cewa "gwamnati wofantar da batun ta kuma maida hankali ga annobar da bata kashe ya kai 2000 ba a fadin kasar."

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa rashin tsaro ya na dada ta'azzara a Kasar, ya roki gwamnati da ta karkatar da biliyan 400 na rigakafin COVID-19 don magance matsalar tsaron.

"Idan na ga matsala, bazan iya shiru ba, saboda idan na yi shiru watakila sauran yan kasa su zarge ni da goyon bayan barna. Amma, maganar gaskiya mu da muke arewa bama jin dadin yadda al'amura ke tafiya.

KU KARANTA: Jerin sunayen shugabannin Amurka da ba suyi tazarce ba

"Ina kallon Najeriya a kasa guda, ba batun shugaba dan arewa, ba wai kawai son zuciyar mu muke fada ba, muna yi a madadin wanda basu samu damar fada ba, na gamsu duk dan kasa yana jin abin da nake ji. A garin mu an kashe kusan mutane 14 cikin kwana biyu, babu tsaro," inji Bafarawa.

Ya bayyana cewa a shekara kusan mutane dubu dari uku ko hudu ne ke mutuwa saboda rashin tsaro a Najeriya.

Mutane kasa da 2000 COVID-19 ta kashe amma an ware biliyan 400 don rigakafi.

Ya bukaci a karkatar da akalar kudin don magance rashin tsaro.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164