Da duminsa: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom ya rasu

Da duminsa: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom ya rasu

- Udo Ekpenyong, shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom ya rasu bayan fama da jinya

- Kamar yadda wani jami'in gwamnatin jihar ya tabbatar, cutar korona ce ta kashe Ekpenyong

- Kafin zamansa shugaban jam'iyyar, ya kasance kwamishinan kananan hukumomi na jihar

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom, Udo Ekpenyong ya rasu.

Ekpenyong ya rasu a ranar Litinin a Uyo kamar yadda wani jami'in gwamnatin jihar Akwa Ibom ya tabbatarwa da Premium Times a ranar Talata da safe.

Jami'in wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce shugaban jam'iyyar PDP din ya rasu ne sakamakon fama da yayi da cutar korona.

KU KARANTA: An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki

Da duminsa: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom ya rasu
Da duminsa: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Akwa Ibom ya rasu. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

Kafin zaben Ekpenyong a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na jihar a shekarar da ta gabata, shine kwamishinan kananan hukumomin da masarautu na jihar. Makusanci ne kuma ga Gwamna Udom Emmanuel.

KU KARANTA: Da duminsa: Allah ya yi wa dan majalisar jiha a Jigawa, Adamu Babban Bare, rasuwa

A wani labari na daban, Allah ya yi wa mai girma sarkin Kauru na jihar Kaduna rasuwa, Alhaji Ja'afaru Abubakar, sakamakon wata 'yar gajeriyar rashin lafiya da yayi.

Ya rasu yana da shekaru 74 a duniya. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya gaji sarautar ne tun 1993.

Ya rasu a asibitin koyarwa na Barau Dikko dake Kaduna a ranar Alhamis da daddare kuma an birne shi a ranar Juma'a a Kauru.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta jagoranci zuwa ta'aziyya ga mutanen karamar hukumar Kauru da 'yan masarautar Kauru a ranar Lahadi.

Wani dan uwa, kuma abokin marigayin, Mallam Sulaiman Lawal (Jarman Kauru) ya kwatanta sarkin a matsayin mutum mai tsoron Allah da kirki, a cewarsa za a yi kewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel