An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki

An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki

- Fusatattun matasan Kafanchan sun bi titin gidan man Ernmaco zuwa ofishin wutar lantarkin Kaduna suna zanga-zanga

- Sun yi zanga-zangar ne sakamakon kara kudin wutar lantarki da aka yi da kuma rashin samun wutar yadda ya kamata bayan canja musu manaja da aka yi

- Ana tsaka da zanga-zangar ne aka harbi wani dalibin GSS Takau dake Kafanchan, daga nan suka cigaba da zanga-zangar nema masa adalci

Fusatattun matasan Kafanchan sun bi titin gidan man Ernmaco zuwa ofishin wutar lantarki na Kaduna suna zanga-zanga akan tashin kudin wuta da kuma rashin samun wutar lantarki yadda ya dace.

Mazauna yankin, wadanda yawanci matasa ne, sun isa har ofishin wutar lantarkin dake Kafanchan rike da takardu wadanda aka rubuta, "A daina amsar kudade masu yawa daga hannunmu, muna bukatar isasasshiyar wuta, a daina barinmu a cikin duhu".

Yayin da Daily Trust ta je wurin an harbi wani dalibin GSS Takau dake Kafanchan, mai suna Noah Ransom a bayansa.

An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki
An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce

An garzaya da Ransom zuwa asibitin Patrick Ibrahim don a kula da lafiyarsa. Wasu daga, cikin matasan sun bayyana wa manema labarai cewa an daga kudin wutar lantarki kuma ba a kai musu isasshiyar wuta, dalilin haka ne yasa suka fita don zanga-zangar lumana.

Sun kara bayyana yadda 'yan Kafanchan suke samun isasshiyar wutar lantarki kafin a canja manajan wutar, amma kuma yanzu an daina kai musu wuta sosai, ga karin kudi da aka yi musu.

Matasan sun bukaci a tsige sabon manajan, don suna zargin shine matsalarsu. Yanzu haka jami'an tsaro suna ta fafutukar dakatar da matasan, yayin da suke nema wa wanda aka harba adalci.

KU KARANTA: Hotunan ministan Buhari yana yawo da sandar guragu sun janyo cece-kuce

An tuntubi jami'in hulda da jama'an 'yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, inda yace bai samu wani cikakken bayani ba akan yadda lamarin ya auku ba, amma ya lashi takobin sanar da yadda abin yake idan ya samu cikakken bayani.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi ya gabatar da motocin alfarma biyu ga sabon Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi domin saukaka masa tafiye-tafiye da al'amuran mulkinsa.

Daya daga cikin motocin akwai kirar SUV Lexus ta 2020 sai wata kirar Toyota Hilux ta 2020.

Babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, Tarfaya Asariya, wanda ya samu rakiyar kwamishinan ayyukan noma, Injiniya Bukar Talba ne suka mika motocin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel