Korona ta yi ajalin likitan Fafaroma Francis

Korona ta yi ajalin likitan Fafaroma Francis

- Fabrizio Soccorsi, likitan da ke duba Fafaroma Francis ya koma ga mahallicinsa

- Soccorsi ya rasu ne sakamakon rashin lafiya mai alaka da cutar coronavirus

- Marigayin ya rasu ne a asibitin Gemelli da ke Rome yana da shekaru 78 a duniya

Fabrizio Soccorsi, likitan Fafaroma Francis ya rasu sakamakon rashin lafiya da ke da alaka da coronavirus, Channels tv ta ruwaito.

A cewar kafar watsa labarai na darikar katolika wacce ta ruwaito abinda jaridar Vatican L’Osservatore Romano ta ruwaito, likitan mai shekaru 78, wadda ake yi wa maganin ciwo mai alaka da 'kansa' ya rasu ne a asibitin Gemelli da ke Rome.

Korona ta yi ajalin likitan Fafaroma Francis
Korona ta yi ajalin likitan Fafaroma Francis. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abinda yasa aka canja na a 'Kwana Casa'in', Safiyya

Soccorsi ya yi karatun likitancinsa ne a Jami'ar Rome La Sapienza.

A watan Agustan 2015, Fafaroma Francis ya nada shi likitansa, bayan kin sabunta wa'addin likitan fafaroma Patrizio Polisca wadda kuma shine shugaban ayyukan lafiya na Vatican.

Tun daga zamanin Fafaroma John Paul II, mutum daya ake bawa mukaman biyu amma Fafaroma Francis ya kauracewa wannan al'adar ya zabi Soccorsi, likitan daga wajen Vatican.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi

A lokacin da ya ke raye, Soccorsi ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa kasashen ketare tare da fafaroma.

A Mayun 2017, a daya daga cikin ziyarce-ziyarce zuwa Fatima, Portugal, Fafaroma Francis ya ajiye furai a gaban gunkin Maryama da nufin addu'ar samawa diyar Soccorsi lafiya, kuma ta rasu bayan wata guda.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164