Kalli yadda dakarun sojin Nigeria suka lallasa Boko Haram da ISWAP (bidiyo)

Kalli yadda dakarun sojin Nigeria suka lallasa Boko Haram da ISWAP (bidiyo)

- Rundunar soji ta yi gagarumin nasara a kan mayakan hadin gwiwa na ISWAP da Boko Haram

- A kan haka, rundunar tsaron ta yi nasarar kwato wani sansanin soji daga yan ta’addan

- A halin da ake ciki, yan ta’addan na ikirarin samun nasara a harinsu kan sojojin

A wani lamari da ya zai faranta ran yan Najeriya da dama, rundunar sojojin kasar ta yi gagarumin nasara ta hanyar lallasa wasu mambobin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Dakarun sun kuma yi nasarar kwato wani sansanin sojoji daga yan ta’addan a karshen mako.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu, yan ta’addan sun kwace Marte, wani gari da ke kilomita 93 daga Maiduguri, babbar birnin jihar Borno, da sansanin sojoji da ke chan.

Kalli yadda dakarun sojin Nigeria suka lallasa Boko Haram da ISWAP (bidiyo)
Kalli yadda dakarun sojin Nigeria suka lallasa Boko Haram da ISWAP (bidiyo) Hoto: @DefenceInfoNG
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: COVID-19: FG ta ce akwai yiwuwar sake kulle kasar a karo na biyu, ta gargadi yan Nigeria

Sakamakon haka, sai dakarun soji suka kai harin bazata kan tawagar yan ta’addan kafin suka kakkabe su.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga jagoran labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Enenche.

Ya ce rundunar sojin sama na Operation lafiya dole ta lalata karin motocin bindiga shida sannan suka shafe yan ta’adda da dama wadanda ke kokarin karfafa takwarorinsu a harin.

Sai dai yan ta’addan na ikirarin wani batu na daban.

A cewar wata sanarwa a shafinsu na Amar news a Telegram, ISIL sun yi ikirarin cewa an kashe mutane bakwai, an kuma kama mutum daya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya amince da nadin Nuhu Fikpo a matsayin shugaban riko na NDE

Yan ta’addan sun kuma yi ikirarin cewa mayakansu sun kwace makamai, alburusai da motoci shida sannan cewa sun kona sansanonin soji.

Babu tabbaci kan wannan ikirari nasu.

A wani labarin, a ranar Lahadi, 17 ga watan Junairu, 2021, rundunar sojojin Operation Hadarin Daji suka kashe ‘yan bindiga 35 a jihar Zamfara inji jaridar Punch.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar sun yi nasarar karbe wasu dabbobi da miyagun suka sace.

Babban jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a Gusau, jihar Zamfara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel