Tsohon ministan Nigeria, Jubril Kuye ya riga mu gidan gaskiya

Tsohon ministan Nigeria, Jubril Kuye ya riga mu gidan gaskiya

- Allah ya yi wa tsohon karamin ministan Kudi da Masana'antu, Sanata Jubril Martins-Kuye

- Tsohon ministan ya rasu ne a gidansa da ke Victoria Garden City a Legas

- Daya daga cikin yayansa ya tabbatar da rasuwar Jubril Kuye kuma ya ce za a tafi da gawarsa garinsu don yi masa jana'iza

Tsohon karamin ministan Kudi da Cinikayya da Masana'antu, Sanata Jubril Martins-Kuye ya rasu yana da shekaru 78 a duniya.

Daya daga cikin yayansa, Bolaji, ya tabbatar wa The Punch rasuwarsa a ranar Lahadi.

Tsohon ministan Nigeria, Jubril Kuye ya riga mu gidan gaskiya
Tsohon ministan Nigeria, Jubril Kuye ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: @MobilePunch
Source: UGC

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa kanwar Janar Sani Abacha rasuwa

Ya ce, "Zan iya tabbatar maka cewa ya rasu a safiyar yau misalin karfe 10.05 na safe. Mun yi bakin cikin rashinsa amma muna gode wa Allah bisa irin rayuwar da ya yi kuma ya taimakawa al'umma.

"Ya rasu yana da shekaru 78 a gidansa da ke Victoria Garden City da ke Legas.

"Mun shirin kai gawarsa garinsu inda muke fatan za ayi masa jana'iza da karfe 4 na yamma bisa koyarwar addinin musulunci."

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya nada shi ministan Cinikayya da Masana'antu a ranar 6 ga watan Afrilun 2010 a lokacin yana shugaban kasa na rikon kwarya.

An haifi marigayi Martins Kuye ne a watan Augustan 1942 a Ago iwoye, a mazabar Ijebu da ke Jihar Ogun. Ya yi karatun digiri na farko a fanin nazarin halayar al'umma wato Sociology a Jami'ar Ibadan (1965-1968) daga nan kuma ya tafi Jami'ar Harvard inda ya yi digiri a bangaren tattalin arziki a 1983. Ya kuma samu shaidar zama Kwararren Akanta.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22

Martins-Kuye sanata ne a Jamhuriya ta Uku.

Martins Kuye ya zama mamba na jam'iyyar United Nigeria Congress Party gabanin karshen mulkin Janar Sani Abacha. Shi ne dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Jihar Ogun a zaben 1999.

An nada shi karamin ministan kudi a Yunin 1999 lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a wa'adinsa na farko inda ya yi aiki har zuwa Yunin 2003.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel