'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22

'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22

- Yan sanda a jihar Zamfara sun yi nasarar ceto mutum takwas daga hannun masu garkuwa

- Yan sandan tare da hadin gwiwa da tubabbun shugabannin yan bindiga sun kwato bindiga da alburusai

- Rundunar yan sandan har wa yau ta yi nasarar kama mutane 22 da ake zargi da aikata laifuka daban daban

'Yan sanda sun ceto mutane takwas daga hannun masu garkuwa a kauyukan Gidan Barga da Dangajeru da ke Kananan hukumomin Tsafe da Talata na jihar yayinda suka kama mutum 22 da ake zargin bata gari ne, The Channels ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar, Abutu Yaro, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya kira a hedkwatan hukumar da ke Gusau a ranar Asabar.

'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22
'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

Yaro ya yi bayanin cewa ana zargin mutane 22 da aka kama da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi, kisan kai da satar mota a sassan jihar.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa kanwar Janar Sani Abacha rasuwa

Ya kuma ce jajircewar na yan sanda ya sa an kwato makamai daga hannun wadanda ake zargin yan bindiga ne.

"Kokarin mu a makonni uku da suka gabata ya sa munyi nasarar kwato AK 47 guda daya da alburusai biyu masu harsashi 18 a karamar hukumar Shinkafi na Jihar Zamfara," a cewar shugaban yan sandan.

"Wannan ya faru ne a ranar 15 ga watan Janairun 2021 a yayin da DPO na Shinkafi tare da hadin gwiwar wasu shugabannin tubabbun yan bindiga a garin suka tabbatar da mika AK 47 daya da kunshin alburusai biyu masu harsashi 18."

A cewar kwamishinan, an samu nasarorin ne tun daga 24 ga watan Disambar 2020 zuwa 14 ga watan Janairu sakamakon jajircewar yan sandan jihar da ke fatattakan yan bindiga.

Ga hotunan a kasa:

'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22
'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Hon. Dimeji Bankole

'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22
'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22. Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

A wani labarin daban, lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel