Zaben kananan hukumomi: APC ta lashe dukkan kujeru 44 na jihar Kano

Zaben kananan hukumomi: APC ta lashe dukkan kujeru 44 na jihar Kano

- Jam'iyya mai mulki a jihar Kano, APC, ta yi nasarar lashe kujerun dukkan kananan hukumomi 44 da aka yi a jihar

- Shugaban hukumar zabe ta jihar Kano mai zaman kanta, Farfesa Sheka, ya tabbatar da hakan yayin bayyana sakamako

- Ya jinjinawa Gwamna Abdullahi da jama'ar jihar a kan yadda suka bada hadin kai har aka samu nasarar yin zaben

Jam'iyya mai mulki ta APC ta lashe dukkan kujerun zaben kananan hukumomi 44 da aka yi a jihar Kano. Jam'iyyar mai mulki ta kara da kwashe dukkan kujerun kansiloli 484 na gundumomi a fadin jihar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, Farfesa Garba Sheka ya bayyana hakan yayin bada sanarwar sakamakon zabukan da aka yi a ranar Asabar.

Farfesa Sheka ya ce an saka kuri'i 2, 350, 577 a yayin zaben. Ya ce duk da kananan kalubalen da aka samu yayin zaben, hukumar ta yi zaben cike da nasarori, Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai

Zaben kananan hukumomi: APC ta lashe dukkan kujeru 44 na jihar Kano
Zaben kananan hukumomi: APC ta lashe dukkan kujeru 44 na jihar Kano. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Farfesa Sheka ya jinjinawa gwamnatin jihar a kan yadda bata saka hannunta ba cikin al'amuran zaben tun farko har zuwa karshe.

Ya kara da jinjinawa jami'an tsaro da dukkan jama'ar jihar da suka bada goyon baya har aka samu yin zaben cike da nasara.

KU KARANTA: Boko Haram: Bam ya tashi da sojoji 5, wasu 15 sun jigata a Borno

An samu rikici a yammacin Juma'a a filin sauka da tashi na jiragen sama na Malam Aminu Kano bayan fasinjoji sun tada tarzoma sakamakon soke tashin jirgin yammacin na kamfanin Azman da aka yi.

Rikicin ya yi kamari wanda ya kai ga wata ma'aikaciyar kamfanin Azman ta yanke jiki ta fadi yayin tashin hankalin.

An bar wani fasinja cikin jini yayin da wani ma'aikacin kamfanin ya kusa tsirara bayan yagalgala masa kaya da aka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel