Kano: An bai wa hammata iska tsakanin fasinjoji da jami'an kamfanin AZMAN

Kano: An bai wa hammata iska tsakanin fasinjoji da jami'an kamfanin AZMAN

- Fasinjoji da jami'an kamfanin AZMAN sun bai wa hammata iska a filin jirgi na Malam Aminu Kano

- Wata ma'aikaciya ta yanke jiki ta fadi yayin da aka yagalgala kayan wani ma'aikaci bayan rikici da fasinjoji

- Hakan ya faru ne bayan kamfanin ya soke tashin jirginsu na yammacin ranar Juma'a babu gamsasshen bayani

An samu rikici a yammacin Juma'a a filin sauka da tashi na jiragen sama na Malam Aminu Kano bayan fasinjoji sun tada tarzoma sakamakon soke tashin jirgin yammacin na kamfanin Azman da aka yi.

Rikicin ya yi kamari wanda ya kai ga wata ma'aikaciyar kamfanin Azman ta yanke jiki ta fadi yayin tashin hankalin.

An bar wani fasinja cikin jini yayin da wani ma'aikacin kamfanin ya kusa tsirara bayan yagalgala masa kaya da aka yi.

Kano: An bai wa hammata iska tsakanin fasinjoji da jami'an kamfanin AZMAN
Kano: An bai wa hammata iska tsakanin fasinjoji da jami'an kamfanin AZMAN. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce

Lamarin ya fara ne bayan fasinjan da za su tashi daga Kano zuwa Legas daga karfe 7:30 zuwa 8:30 suka gane an soke tafiyarsu.

Fasinjojin da ke tafiya daga Kano zuwa Abuja su ma hakan suke fuskanta a wannan lokacin da lamarin ke faruwa.

Daily Trust ta gano cewa irin haka ta faru a daren Alhamis yayin da ake sa ran tashin jirginsu na karfe 8:15 na yammaci daga Abuja zuwa Kano.

Kamfanin jirgin saman sun soke tashin jirgin ba tare da bada hakuri ba ga fasinjojin.

Fasinjojin sun fusata inda suka fara bukatar amsa amma babu mai saurarensu. Ba a basu wurin kwana ba ko kuma yadda za su mayar da kansu gida ba.

Wata fasinja mace a ranar Juma'a tana kuka ta sanar da Daily Trust cewa bikin aurenta ne za a yi ranar Asabar a Abuja amma an soke tafiyarta. Bata san yadda za ta iya isa Abuja ba kafin Asabar.

KU KARANTA: Yadda jihohi 27 suka tirsasa gwamnatin tarayya bude makarantu

A wani labari na daban, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce 'yan Najeriyan da suka ki mika lamurran harkar tsaro a hannun Ubangiji, suna da matsala, kuma su na cigaba da jan yaki akan ta'addanci.

Adesina ya bayyana hakan ne a wata takarda ta ranar Alhamis. Hadimin shugaban kasan ya lura da wani bidiyo wanda ya yi ta yawo na wani soja da wasu mutane 4 suna waka, wacce suke cewa nasara daga Ubangiji kadai take.

Adesina ya ce 'yan Najeriya da dama sun kasa fahimtar cewa nasara daga Ubangiji kadai take, The Punch ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel