Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai

Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai

- Wani mutum mai amfani da suna Prophet Mufasa ya bayyana irin matar da yake da burin aure

- A cewarsa, wajibi ne ta zama tana matukar tsoronsa, don idan ta bata masa rai, ta mutu kawai

- Bincike ya bayyana cewa ya goge shafin nasa na Twitter don caccakar da mutane suka fara masa

Wani mutum ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya bayyana irin yanayin matar da yake son ya aura.

A cewarsa, wajibi ne matarsa ta zama mai matukar tsoronsa. Prophet Mufasa ya ce ba zai taba auren matar da bata tsoronsa ba.

Mufasa ya ce wajibi ne ta san cewa idan ta bata masa rai, sai ta mutu.

Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai
Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai. Hoto daga @ProphetMufasa
Asali: Instagram

KU KARANTA: Sojin sama sun yi wa Boko Haram ruwan wuta, sun halaka 'yan ta'adda a Borno

Kamar yadda ya wallafa, "Wajibi ne wacce zan aura ta dinga tsorona, don ta san cewa indai har ta bata masa rai, rayuwarta ta zo karshe."

Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai
Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai. Hoto daga Roos Koole
Asali: Getty Images

Mutane da dama sun hau caccakarsa, har wata nnachod tace: "Maza masu irin wannan tunanin basu cancanci su yi soyayya ba. Maimakon ka nemi matarka ta girmama ka, sai ka nemi tsoro."

Wani officialmubaba cewa yayi: "Kaje ka auri kanwarka".

KU KARANTA: 'Yan fashi da makami sun bindige wani bawan Allah a garin Kano

Jenniferunachukwu cewa tayi, "Wata macen sai ta ga wannan wallafar ta kwashi dariya ta cigaba da soyayya dashi."

Oficial_olayinkaa yace: "Kai kuwa dabba ne? Maimakon ka auri kawarka?"

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Katsina sun kama wani Kabiru Bashir mai shekaru 27 da Sadiq Ashiru mai shekaru 30, duk 'yan karamar hukumar Danbatta dake jihar Kano bisa zargin damfarar mutane ta waya da sunan su Aljanu ne.

Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya sanar da hakan a wata takarda, wacce yace alhakin jama'a ne ya kama su bayan sun amshi katin bankin wata Rabi'atu Garba ta karamar hukumar Mani dake jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel