Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya

Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya

- Najeriya tana da Sarakuna masu arziki da tarin dukiya, kuma Idan ka dubi fadarsu, za ka gane hakan

- A gaba daya Afirka, Sarakunan Najeriya suna cikin Sarakuna masu fada masu kyawun tsari da burgewa

- An kawata fadojin da kasaitattun gine-gine da ado iri-iri, wasu na zamani, wasu kuma dadaddu ne

Najeriya tana da sarakuna masu tarin arziki da daraja a nahiyar Afirka. Sai dai fadojinsu ne suke bayyana hakan.

1. Fadar sarkin Zazzau

Fadar sarkin zazzau da take cikin jihar Kaduna. Yanayin tsarin gine-ginen na 'Habe' ne, kuma an yi mata ado da tambari irin na sarauta.

Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya
Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya. Hoto daga Nairaland.com
Source: UGC

2. Fadar sarkin Musulmi na Sokoto

Kamar yadda tarihi ya bayyana, an samu daular Sokoto ne daga jihadin Shehu Usman Danfodio, tun alif na 19 da 'yankai.

Sultan ne yake sarautar masarautar, kuma shi ne shugaban kaf musulman Najeriya.

Sarkin da ke kan kujerar shine Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar III, kuma shine Sultan na Sokoto na 20. Birgediya janar ne shi na sojojin Najeriya, kafin ya gaji dan uwansa da ya rasu, Sultan Muhammadu Maccido da yayi hatsarin jirgin sama a ranar 29 ga watan Oktoban 2006 a Abuja.

Hakika fadar sarkin ta kasaita, an samu hoton cikin fadar ne, ba wajenta ba.

KU KARANTA: Shugabancin kasa: Kakakin majalisa yana nemawa Gwamna Yahaya Bello goyon baya

3. Fadar Oba na Benin

Fadar tana tsakiyar jihar Benin. Fadar ta kasaita kwarai, sai dai mutum ya kalli iya kallonsa.

Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya
Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya. Hoto daga Nairaland.com
Source: UGC

4. Fadar Ooni na Ife

Fadar tana nan tun 500BC, don dadaddiyar fada ce. An gina fadar ne a tsakiyar Benin, wanda aka fi sani da Enuwa a Ile-Ife.

Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya
Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya. Hoto daga Nairalnad.com
Source: UGC

5. Gidan Rumfa

Fadar Sarkin Kano, wacce aka fi sani da Gidan Rumfa, ta kasaita kwarai. Ita ce fada mai daraja ta biyu ga musulmai idan aka cire ta Sultan din Sokoto.

6. Fadar Obi na Onitsha

Fadar tana Onitsha, tsakiyar wurin hada-hadar kasuwanci a jihar Anambra. Wannan ce fadar Igwe Nnaemeka Achebe, Obi na Onitsha.

Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya
Kyawawan hotunan fadar sarakuna 6 mafi kasaita a fadin Najeriya. Hoto daga Nairaland.com
Source: UGC

KU KARANTA: Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce

A wani labari na daban, wani mutum ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya bayyana irin yanayin matar da yake son ya aura.

A cewarsa, wajibi ne matarsa ta zama mai matukar tsoronsa. Prophet Mufasa ya ce ba zai taba auren matar da bata tsoronsa ba.

Mufasa ya ce wajibi ne ta san cewa idan ta bata masa rai, sai ta mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel