Uwargidan El-Rufai ta koka da yadda wahalar mulki ta mayar da mijinta

Uwargidan El-Rufai ta koka da yadda wahalar mulki ta mayar da mijinta

- Surutai sun fara yawa bayan matar Nasir El-Rufai ta wallafa hotonta da gwamnan a kafar sada zumunta

- Uwargidan gwamnan ta yi korafi akan yanayin yadda gwamnan ya tsufa, duk da shekarunsu daya dashi

- A cewar matar, wahala da matsalolin jihar Kaduna ne suka sanya masa furfurar dake kansa

Hadiza, matar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta bayyana alhininta akan yadda gashin dake kan mijinta ya yi furfura cikin kankanin lokaci.

Uwargidan gwamnan ta wallafa hakan ne a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Asabar, 9 ga watan Janairu.

Hadiza ta wallafa wani hotonsu, wanda suka dauka ita da mijinta cike da shaukin soyayya.

Ta alakanta furfurar mijinta da wahalhalun jihar Kaduna, bayan ta bayyana cewa shekarunsu daya, amma kuma ya fi ta tsufa.

Uwargidan El-Rufai ta koka da yadda wahalar mulki ta mayar da mijinta
Uwargidan El-Rufai ta koka da yadda wahalar mulki ta mayar da mijinta. Hoto daga @hadizel
Source: Twitter

KU KARANTA: Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce

Wannan wallafar ta janyo cece-kuce iri-iri a Twitter, inda mutane da dama suka yi ta yabawa da irin kokarin da gwamnan yake yi wa jihar.

Wata Haleem_Bea ta yi tsokaci da: "Duk wanda ya iya mulkar jihar Kaduna, zai iya mulkar Najeriya, saboda matsalolin bangaranci da na yarukan dake jihar."

Wani Legit_KBawa ya rubuta: "Duk wanda zai iya mulkar jihar Kaduna, zai iya mulkar Najeriya. Malam ya dace ya tsaya takarar shugabancin kasan Najeriya a 2023."

estherclimate shawara ta bayar, inda tace ya dinga shan kayan marmari da motsa jikinsa.

KU KARANTA: Matashi ya ce ba zai iya auren matar da bata tsoronsa ba, ya bayyana kwararan dalilai

A wani labari na daban, kakakin majalisar jihar Kogi, Prince Mathew Kolewole, yana yi wa gwamna Yahaya Bello kamfen don mutane su mara masa baya ya tsaya takarar shugabancin kasar Najeriya a 2023.

Kolawole ya sanar da hakan a Jos, lokacin da ya kai wa kakakin majalisar jihar Filato ziyara, Abok Ayuba da abokan aikinsa don su goyi bayan Bello.

Mataimakinsa, Ahmed Mohammed da sauran 'yan majalisar jihar Kogi ne suka raka shi, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel