Bidiyon Dino Melaye yana kwasar rawar wakar kungiyar maza marowata

Bidiyon Dino Melaye yana kwasar rawar wakar kungiyar maza marowata

- Alamu na nuna kungiyar maza matsolaye na cigaba da shahara ba ga samari kadai ba

- SanataDino Melaye ba a bar shi a baya ba domin kuwa yayi wuff ya fada wannan kungiya

- Ya wallafa bidiyonsa yana kwasar rawa bayan ya saka wakar da ake kira da taken kungiya

Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya shiga kungiyar maza matsolaye da aka kafa kwanan nan, The Nation ta wallafa.

Ya wallafa bidiyonsa yana bin waka tare da cashe rawar wakar da ake kira da wakar kungiya mai suna Simple Man by Nature wacce Oliver De Coque ya rera.

Ya yi wallafa a kasan bidiyon inda yace: "Na ji an ce wannan ce taken kungiyar maza marowata ta Najeriya (SMAN). Da gaske ne?"

Bidiyon Dino Melaye yana kwasar rawar wakar kungiyar maza marowata
Bidiyon Dino Melaye yana kwasar rawar wakar kungiyar maza marowata. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Fitattun mawaka da jama'a a Najeriya sun kafa wata kungiyar maza masu rowa da ake kira da Stingy Men Association of Nigeria.

Kungiyar dai babu shakka ta samu matukar karbuwa a shafukan Facebook da Twitter a Najeriya.

Mawaki Don Jazzy ba a bar shi a baya ba domin kuwa ya wallafa hoton katinsa na zama cikakken dan kungiya, lamarin da yasa jama'a suka dinga wallafawa.

KU KARANTA: Liyafar badala: 'Yan sanda sun damke samarin da ake da shiryawa a Bauchi

KU KARANTA: Mashahurin mai kudin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $14 biliyan a rana daya

A wani labari na daban, jarumar fina-finan kudu, Rita Daniels ta fada cikin matsanancin farin ciki bayan da diyarta Regina Daniels ta gwangwajeta da kyautar alfarma.

A wata wallafa da jaruma Regina tayi tare da tausasan kalami, ta bayyana motar da ta bai wa mahaifiyarta kyauta mai darajar miliyan 15 a matsayin kyautar ranar zagayowar haihuwarta.

A sakon taya mahaifiyarta murnar zagayowar ranar haihuwarta, ta bayyana cewa tana alfahari domin kuwa ta siya motar ne da kudinta wanda ta samu da kanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel