Hotunan Buhari yana rabawa yara kudi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya,kalli abunda yan Nigeria ke kiran Shugaban kasar
Yan Najeriya a shafin soshiyal midiya sun yi martani na ban dariya yayinda hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari yana rabawa kananan yara kudi ya bayyana a yanar gizo.
Legit.ng ta tattaro cewa hotunan ya bayyana a shafin soshiyal midiya a yayinda ake tsaka da kafa kungiyar maza marowata na Najeriya wato Stingy Men Association of Nigeria (SMAN).
An kafa kungiyar ne saboda mazan da suka yi tawaye tare da gajiya da baiwa takwarorinsu mata kudi.
Koda dai abun ya fara ne da masu amfani da shafin soshiyal midiya kadan, an tattaro cewa a yanzu ya samu goyon bayan manyan maza da dama a bangaren nishadantarwa inda suke amfani da muryoyinsu wajen shelata kungiyar.
KU KARANTA KUMA: 2023: Tsohon gwamnan Kano ya bukaci arewa da ta mutunta tsarin mulkin karba-karba
Da ganin Shugaba Buhari yana rabawa kowanne daga cikin yaran kudi yar N500 bibbiyu, wasu yan Najeriya a shafin soshiyal midiya sun bashi gurbi daban-daban a karkashin kungiyar marowatan.
Bunmi Victor Fasae, @bunmifasae, ta bayyana a shafin Twitter cewa Shugaba Buhari ne Shugaban kungiyar SMAN.
Chidubem Ferdinand Atuokoye, @Trinity_Don_JFK, ya ce:
“Kayi tunanin ziyartan Shugaban kasarku sai yayi maka kyautar N1000, menene zai zama martaninka??”
Da yake martani, @IbrahimJafr ya ce Shugaba Buhari ne ma’assashin SMAN.
A martaninsa, @HOOricane ya bayyana Shugaban kasa a matsayin uban kungiyar SMAN.
Wani mai amfani da Twitter, @WizdraqueCK harda yiwa shugaba Buhari katin shaida yayi, cewa shine majibancin kungiyar.
Hakazalika, @KhamisAbdulrauf ya bayyana shugaban kasar a matsayin majibanin SMAN tare da yi masa katin shaida.
KU KARANTA KUMA: Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji
Adenekan Mayowa, @Mayorspeaks, ya ce:
“Shugaba Buhari ya tabbatar da kasancewarsa dan kungiyar marowata, SMAN tunda an dauke shi yana rabawa yara #1,000”
A wani labarin, Hadiza, matar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta bayyana alhininta akan yadda gashin dake kan mijinta ya yi furfura cikin kankanin lokaci.
Uwargidan gwamnan ta wallafa hakan ne a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Asabar, 9 ga watan Janairu.
Hadiza ta wallafa wani hotonsu, wanda suka dauka ita da mijinta cike da shaukin soyayya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng