Allah ya yi wa kanwar Janar Sani Abacha rasuwa
- Hajiya Fanta, kanwar tsohon shugaban mulkin soja ta Najeriya Janar Sani Abacha ta rasu
- Marigayiyar ta rasu ne a wani asibiti a birnin tarayya Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa iyalanta da al'ummar Kano ta'aziyya tare da adduar Allah ya saka mata da aljanna firdausi
Hajiya Fatima Mohammed (Fanta), kanwar tsohon shugaban kasar mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha ta rasu tana da shekaru 75 a duniya.
Ta rasu ne bayan gajeruwar jinya a wani asibiti da ke birnin tarayya, Abuja.
Majiyoyi daga iyalan ta sun ce za a yi mata jana'iza a Kano a ranar Lahadi.
Marigayiyar ce mahaifiyar Basheer Mohammed, Kwamishina a Hukumar Kula da Yan Gudun Hijira da Wadanda suka rasa muhallansu.
DUBA WANNAN: Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Hon. Dimeji Bankole
Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa bisa rasuwarta cikin wani sako da kakakinsa ya fitar inda ya ce marigayiyar mace ce mai tausayi da jin kai da taimakawa marasa karfi.
KU KARANTA: Boko Haram bata da iko akan ko wani gari, Enenche
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Bashir Ahmad ya fitar a ranar Asabar ta ce, Buhari yana yi wa iyalan Abacha, Mista Mohammed da yan uwansa da al'ummar Jihar Kano ta'aziyyar rasuwarta.
Ya ce Hajiya Fanta ta sadaukar da rayuwarta a duniya wurin kulawa da gajiyayyu da yi wa yaranta tarbiyya na gari.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi addu'ar Allah ya bawa dukkan yan uwa da abokan ta hakurin rashi ya kuma saka mata da gidan aljanna Firdausi.
A wani labarin daban, lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.
Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng