Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Hon. Dimeji Bankole

Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Hon. Dimeji Bankole

- Tsohon kakakin majalisar tarayyar Najeriya, Dimeji Bankole ya auri yar gwamnan Kebbi, Aisha Shinkafi Sa'idu

- An daura auren ne a ranar Juma'a 15 ga watan Janairun 2020 a babban birnin tarayya Abujan Najeriya

- Manyan mutane da dama sun hallara wurin taron ciki har da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara

An daura aure tsakanin tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dimeji Bankole da sahibarsa, Aisha Shinkafi Sa'idu, diyar gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu a birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a 15 ga watan Janairu.

Bankole ya rabu da tsohuwa matarsa ne tun a shekarar 2017, daga bisani ya fara soyayya da Aisha, wacce lauya ce da ta yi karatunta a Jami'ar Hull da ke Birtaniya.

DUBA WANNAN: Yan fashi sun tilastawa maigida kwanciya da matarsa yayinda suka nadi bidiyo

Manyan mutane da dama sun samu hallartar bikin cikinsu har da tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayya, Yakubu Dogara.

Bisa dukkan alamu bikin ya yi armashi duba da yadda mahalarta taron suke cikin annashuwa da murna a hotunan da aka dauka yayin bikin.

Kamar yadda aka saba ganinsa, Ango Dimeji Bankole ya sanya fararen tufafi ne fa farar hula yayin da amarya kuma ta saka tufafi mai lauyin da ya yi kama da ruwan dorawa.

Abokan ango su kuma sun saka fararen tufafi da huluna masu lauyin shudi.

Ga hotunan a kasa:

Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole
Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole
Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Jam'iyyun siyasa 30 sun juya wa Fintiri baya, za su marawa Ardo baya

Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole
Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole
Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole
Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Dimeji Bankole. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel