Shugabancin kasa: Kakakin majalisa yana nemawa Gwamna Yahaya Bello goyon baya

Shugabancin kasa: Kakakin majalisa yana nemawa Gwamna Yahaya Bello goyon baya

- Kakakin majalisar jihar Kogi, Prince Mathew Kolewole, ya jagoranci sauran 'yan majalisar jihar zuwa jihar Filato

- Sun je ne har wurin kakakin majalisar jihar Filato, Abok Ayuba, don yi wa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kamfen

- Sun nemi goyon bayansa da kuma wadanda suke karkashinsa don Yahaya Bello ya tsaya takarar shugabancin kasar Najeriya a 2023

Kakakin majalisar jihar Kogi, Prince Mathew Kolewole, yana yi wa gwamna Yahaya Bello kamfen don mutane su mara masa baya ya tsaya takarar shugabancin kasar Najeriya a 2023.

Kolawole ya sanar da hakan a Jos, lokacin da ya kai wa kakakin majalisar jihar Filato ziyara, Abok Ayuba da abokan aikinsa don su goyi bayan Bello.

Mataimakinsa, Ahmed Mohammed da sauran 'yan majalisar jihar Kogi ne suka raka shi, Daily Trust ta ruwaito.

Shugabancin kasa: Kakakin majalisa yana nemawa Gwamna Yahaya Bello goyon baya
Shugabancin kasa: Kakakin majalisa yana nemawa Gwamna Yahaya Bello goyon baya. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina

"Mun zo ne don mu taya kakakin majalisar Filato Abok Ayuba murna, sakamakon zabensa da aka yi a matsayin shugaban kungiyar kakakan majalasun jihohin arewa ta tsakiya na Najeriya.

"Mun kuma zo ne don mu nemi goyon bayanku don ku mara wa mai girma Alhaji Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi baya ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2023, don shi ne gwamna mafi karancin shekaru a Najeriya.

"Yanayin yadda gwamnanmu yake mu'amala da mu a matsayinmu na 'yan majalisa, mun yaba kwarai da jajircewarsa akan harkar tsaro, taimakon mata, bai wa matasa muhimmanci, ilimi da kuma bunkasa ma'aikatu.

KU KARANTA: Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin

"Mun yaba da shi, kuma mun ga yadda yake tafiyar da ayyukansa yadda ya kamata.

"Sakamakon haka, mun yanke shawarar tabbatar masa da samun nasara, muna kuma bukatar ya tsaya takarar shugabancin Najeriya."

A cewarsu, Najeriya tana bukatar mutum mai jini a jikinsa kamar Yahaya Bello. Kuma 'yan majalisar jihohin Najeriya sun kai 988, cikinsu kuma 600 'yan jam'iyya APC ne.

Ayuba ya tabbatar da cewa 'yan majalisar Filato za su mara masa baya dari bisa dari, kuma zai tabbatar ya isar da sakonsu zuwa 'yan majalisar.

A wani labari na daban, rundunar Operation Lafiya Dole a ranar Talata ta ragargaza mayakan ta'addanci na Boko Haram kuma sun lalata motcoin yakin 'yan ta'addan a wani samame da suka kai ta jiragen yaki a Mainok da ke Borno, hedkwatar tsaro tace.

Shugaban fannin yada labarai an tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Enenche ya ce an kai harin ne bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya nuna cewa 'yan bindigan na kai kawo a Jakana-Mainok na jihar da motocin yaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel